Sharon
An kuma san shi da: Saron
32.6300, 34.9400 Duba a Google Maps
Ayoyin da suka ambaci Sharon
Shitrai mutumin Sharon shi ne mai lura da garkuna masu kiwo a Sharon. Shafat ɗan Adlai shi ne mai lura da garkuna a kwari.
Ni furen bi-rana ne na Sharon, furen bi-rana na kwari.
Ƙasa tana kuka an kuma gudu an bar ta, Lebanon ta sha kunya ta kuma yanƙwane; Sharon ta zama kamar Araba, Bashan da Karmel sun kakkaɓe ganyayensu.
zai buɗu ya hudo; zai yi farin ciki mai girma ya kuma yi sowa don farin ciki. Za a maido wa Lebanon da darajarta, darajar Karmel da Sharon; za su ga ɗaukakar Ubangiji, darajar Allahnmu.
Sharon zai zama wurin kiwo don shanu, Kwarin Akor kuma wurin hutun garkuna, domin mutanena da suke nemana.
Duk waɗanda suke zama a Lidda da Sharon suka gan shi suka kuma juyo ga Ubangiji.