Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Valleys

83 ayoyi · 58 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Dukan waɗannan sarakuna na bayan nan suka haɗa kai a Kwarin Siddim (Teku Gishiri).

  2. Sai sarkin Sodom, sarkin Gomorra, sarkin Adma, sarkin Zeboyim da sarkin Bela (wato, Zowar), suka fita suka ja dāgā a Kwarin Siddim

  3. Bayan Abram ya dawo daga cin Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi a yaƙi, sai sarkin Sodom ya fito don yă tarye Abram a Kwarin Shabe (wato, Kwarin Sarki).

  4. Saboda haka Ishaku ya fita daga can, ya yi sansani a Kwarin Gerar, ya kuma zauna a can.

  5. Saboda haka Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Jeka ka ga ko kome lafiya yake da ’yan’uwanka da kuma garkunan, ka kawo mini labari.” Sa’an nan ya sallame shi daga Kwarin Hebron. Sa’ad da Yusuf ya kai Shekem,

  6. Daga nan kuma suka ci gaba, suka yi sansani a Kwarin Zered.

  7. “Kamar kwaruruka suke a shimfiɗe, kamar lambu kusa da rafi, kamar itatuwan aloyes da Ubangiji ya dasa, kamar itatuwa al’ul kusa da ruwaye.

  8. Gama bayan suka haura Kwarin Eshkol suka hangi ƙasar, sai suka karya zuciyar Isra’ilawa daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su.

  9. Ku tashi, ku ci gaba zuwa ƙasar tudun Amoriyawa; ku tafi wurin dukan maƙwabta a cikin Araba, a cikin duwatsu, a gindin yammancin tuddai, a Negeb da kuma a ta kwaruruka, da ƙasar Kan’aniyawa da kuma zuwa Lebanon, har zuwa babban kogi, wato, Yuferites.

  10. Suka tafi, suka haura zuwa ƙasar tudu, suka kai Kwarin Eshkol, suka leƙo asirin ƙasar.

  11. Gama Ubangiji Allahnku yana fitar da ku zuwa cikin ƙasa mai kyau, ƙasa mai rafuffuka da tafkunan ruwa, tare da maɓulɓulai masu gudu a kwari da tuddai;

  12. Amma ƙasar da kuke haye Urdun ku mallaki, ƙasa ce ta duwatsu da kwaruruka wadda ruwan sama ne yake jiƙe ta.

  13. a gangara da ita kwarin da ba a taɓa nome, ko shuki a ciki ba, inda kuma akwai rafi mai gudu, a can cikin kwarin za su karye wuyanta.

  14. da Negeb da dukan yankin Kwarin Yeriko, Birnin Dabino, har zuwa Zowar.

  15. Aka binne shi a Mowab, a kwarin kusa da Bet-Feyor, amma har wa yau babu wanda ya san inda kabarinsa yake.

  16. Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka ɗauki Akan ɗan Zera, da azurfar, doguwar rigar, sandan zinariya, ’ya’yansa maza da mata, shanunsa, jakuna da tumaki, tentinsa da duk abin da yake da shi, suka kai su Kwarin Akor.

  17. A ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa a hannun Isra’ilawa, Yoshuwa ya ce wa Ubangiji a gaban Isra’ilawa, “Ke rana, ki tsaya cik a Gibeyon Kai wata, ka je Kwarin Aiyalon.”

  18. Yoshuwa ya cinye yankin duka da yaƙi, haɗe da na kan tudu, da Negeb, da kwarin yamma, da filayen cikin duwatsu tare da sarakunansu duka. Bai bar wani da rai ba, ya kashe duk wani mai numfashi, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ilawa ya umarta.

  19. Daga Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa wajajen Seyir, zuwa Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon ƙasa da Dutsen Hermon. Ya kama sarakunansu ya karkashe su.

  20. Sai kuma ta gangara zuwa Kwarin Ben Hinnom a gangaren kudancin birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima). Daga can ta haura zuwa kan tudun a yammancin Kwarin Hinnom, a arewancin ƙarshen Kwarin Refayim.

  21. Iyakar ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskantar Kwarin Ben Hinnom, wanda yake arewa da Kwarin Refayim. Ta ci gaba ta gangara ta Kwarin Hinnom ta yi kudu kusa da birnin Yebusiyawa har zuwa En Rogel.

  22. Waɗannan su ne garuruwan da kabilar Benyamin suke da su na gādo. Yeriko, Bet-Hogla, Emek Keziz,

  23. A can ne iyakar ta kewaya zuwa Hannaton, sa’an nan ta ƙarasa a Kwarin Ifta El.

  24. Sai ta yi gabas zuwa Bet-Dagon, ta taɓa Zebulun da kuma Kwarin Ifta El, ta wuce arewa zuwa Bet-Emek da Neyiyel, ta wuce Kabul a hagu,

  25. Ubangiji kuwa yana tare da mutane Yahuda. Suka mallaki ƙasar tudu, amma ba su iya suka kori mutanen daga filaye ba, domin suna da keken yaƙin ƙarfe.