Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Allegory

22 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Wata rana itatuwa suka fita don su naɗa wa kansu sarki. Suka ce wa itacen zaitun, ‘Ka zama sarkinmu.’

  2. “Amma itacen zaitun ya ce, ‘In bar mai nawa, wanda da shi ake girmama alloli da mutane, don in zo in yi ta fama da itatuwa?’

  3. “Biye da wannan, sai itatuwan suka ce wa itacen ɓaure, ‘Zo ka zama sarkinmu.’

  4. “Amma itacen ɓauren ya ce, ‘In bar kyawawan ’ya’yana da zaƙinsu, in zo in yi ta fama da itatuwa?’

  5. “Sa’an nan itatuwan suka ce wa kuringar inabi, ‘Ki zo ki zama sarkinmu.’

  6. “Amma kuringar ta ce, ‘In bar ruwan inabina, wanda yake faranta zuciyar alloli da mutane, in zo in yi fama da itatuwa?’

  7. “A ƙarshe sai dukan itatuwa suka ce wa itacen ƙaya, ‘Ka zo ka zama sarkinmu.’

  8. “Itacen ƙaya ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske ne kuke so ku naɗa ni sarkinku, ku zo ku sha inuwana; in ba haka ba, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al’ul na Lebanon!’

  9. Kyarkeci zai zauna tare da ɗan rago damisa za tă kwanta tare da akuya, ɗan maraƙi da zaki da ɗan saniya za su yi kiwo tare; ɗan yaro ne zai lura da su.

  10. Saniya da beyar za su yi kiwo tare, ƙananansu za su kwanta tare, zaki kuma zai ci ciyawa kamar saniya.

  11. Jariri zai yi wasa kurkusa da ramin gamsheƙa, ɗan yaro kuma zai sa hannunsa a ramin maciji mai mugun dafi.

  12. Hamada da ƙeƙasasshiyar ƙasa za su yi murna; jeji zai yi farin ciki ya kuma hudo. Kamar fure,

  13. zai buɗu ya hudo; zai yi farin ciki mai girma ya kuma yi sowa don farin ciki. Za a maido wa Lebanon da darajarta, darajar Karmel da Sharon; za su ga ɗaukakar Ubangiji, darajar Allahnmu.

  14. Ku ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi, ku ƙarfafa gwiwoyin da suka gaji;

  15. ku faɗa wa waɗanda suka karai a zukata, “Ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro; Allahnku zai zo, zai zo domin ya ɗau fansa; da ramuwar Allah zai zo don yă cece ku.”

  16. Sa’an nan idanun makafi za su buɗe kunnuwan kurame kuma su ji.

  17. Sa’an nan guragu za su yi tsalle kamar barewa, bebaye kuma su yi sowa don farin ciki. Ruwa zai kwararo daga jeji rafuffuka kuma a cikin hamada.

  18. Yashi mai ƙuna zai zama tafki, ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za tă cika da maɓulɓulan rafuffuka. A mazaunin diloli, inda suka taɓa zama, ciyawa da iwa da kyauro za su yi girma.

  19. Kuma babbar hanya za tă kasance a can; za a ce ta ita Hanyar Mai Tsarki. Marasa tsarki ba za su yi tafiya a kanta ba; za tă zama domin waɗanda suka yi tafiya a wannan Hanya ce; mugaye da wawaye ba za su yi ta yawo a kanta ba.

  20. Zaki ba zai kasance a can ba, balle wani naman jeji mai faɗa ya haura kanta; ba za a same su a can ba. Amma fansassu ne kaɗai za su yi tafiya a can,

  21. kuma fansassu na Ubangiji za su komo. Za su shiga Sihiyona da rerawa; matuƙar farin ciki zai mamaye su. Murna da farin ciki za su sha kansu, baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.

  22. Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ’ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan.