Skip to content

Hagar

12 ayoyi · 2 'yan gida

An kuma san shi da: Agar

Ayoyin da suka ambaci Hagar

  1. To, Saira, matar Abram, ba tă haifa masa ’ya’ya ba. Amma tana da wata baiwa mutuniyar Masar mai suna Hagar,

  2. Saboda haka bayan Abram ya yi zama a Kan’ana shekaru goma, Saira matarsa ta ɗauki Hagar baiwarta ta ba wa mijinta tă zama matarsa.

  3. Abram kuwa ya kwana da Hagar, ta kuma yi ciki. Sa’ad da Hagar ta gane tana da ciki, sai ta fara rena uwargijiyarta.

  4. Ya kuma ce mata, “Hagar, baiwar Saira, daga ina kika fito, kuma ina za ki?” Ta amsa ta ce, “Ina gudu ne daga wurin uwargijiyata Saira.”

  5. Haka fa Hagar ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya ba da suna Ishmayel ga ɗan da ta haifa.

  6. Abram yana da shekaru 86 sa’ad da Hagar ta haifa masa Ishmayel.

  7. Amma Saratu ta ga cewa yaron da Hagar, mutuniyar Masar ta haifa wa Ibrahim yana wa ɗanta Ishaku gori,

  8. Kashegari da sassafe sai Ibrahim ya ɗauki abinci da salkar ruwa, ya ba wa Hagar. Ya ɗora su a kafaɗunta, sa’an nan ya sallame ta da yaron. Ta kama hanyarta ta kuma yi ta yawo a cikin jejin Beyersheba.

  9. Allah kuwa ya ji yaron yana kuka, sai mala’ikan Allah ya kira Hagar daga sama ya ce mata, “Mene ne damuwarki, Hagar? Kada ki ji tsoro, Allah ya ji yaron yana kuka yayinda yake kwance a can.

  10. Waɗannan su ne zuriyar Ishmayel ɗan Ibrahim, wanda Hagar mutuniyar Masar, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.

  11. Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ’ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan.

  12. Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima na yanzu, gama ita baiwa ce tare da ’ya’yanta.