Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Hagar

10 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Waɗannan su ne zuriyar Ishmayel ɗan Ibrahim, wanda Hagar mutuniyar Masar, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.

  2. Ga jerin sunayen ’ya’yan Ishmayel maza bisa ga haihuwarsu, Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam,

  3. Mishma, Duma, Massa,

  4. Hadad, Tema, Yetur, Nafish da Kedema.

  5. Suka yi yaƙi da Hagirawa, Yetur, Nafish da Nodab.

  6. Aka taimake su a yaƙin, Allah kuma ya ba da Hagirawa da dukan abokansu gare su, domin sun yi kuka gare shi a lokacin yaƙin. Ya amsa addu’o’insu, domin sun dogara gare shi.

  7. Suka ƙwace dabbobin Hagirawa, raƙuma dubu hamsin, tumaki dubu ɗari biyu da hamsin da kuma jakuna dubu biyu. Suka kuma kame mutane dubu ɗari ɗaya,

  8. waɗansu suka mutu, domin yaƙin na Allah ne. Suka zauna a ƙasar har lokacin da aka kai su zaman bauta.

  9. Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ’ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan.

  10. Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima na yanzu, gama ita baiwa ce tare da ’ya’yanta.