Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Achor

4 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Suka tara manyan duwatsu a kan Akan, tarin duwatsun na nan a can har wa yau. Sa’an nan Ubangiji ya huce daga fushinsa mai zafi. Saboda haka ake kiran wurin Kwarin Akor.

  2. Sai iyakar ta haura zuwa Debir daga Kwarin Akor ta juya arewa da Gilgal, wadda take fuskantar hawan Adummim a kudancin kwari, ta ci gaba zuwa ruwan En Shemesh, ta ɓullo ta En Rogel.

  3. Sharon zai zama wurin kiwo don shanu, Kwarin Akor kuma wurin hutun garkuna, domin mutanena da suke nemana.

  4. A can zan mayar mata da gonakin inabinta, zan kuma sa Kwarin Akor yă zama ƙofar bege. A can za tă rera kamar a kwanakin ƙuruciyarta, kamar a lokacin da ta fita daga Masar.