Skip to content

Achor

5 verses

31.8300, 35.3900 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Achor

  1. Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka ɗauki Akan ɗan Zera, da azurfar, doguwar rigar, sandan zinariya, ’ya’yansa maza da mata, shanunsa, jakuna da tumaki, tentinsa da duk abin da yake da shi, suka kai su Kwarin Akor.

  2. Suka tara manyan duwatsu a kan Akan, tarin duwatsun na nan a can har wa yau. Sa’an nan Ubangiji ya huce daga fushinsa mai zafi. Saboda haka ake kiran wurin Kwarin Akor.

  3. Sai iyakar ta haura zuwa Debir daga Kwarin Akor ta juya arewa da Gilgal, wadda take fuskantar hawan Adummim a kudancin kwari, ta ci gaba zuwa ruwan En Shemesh, ta ɓullo ta En Rogel.

  4. Sharon zai zama wurin kiwo don shanu, Kwarin Akor kuma wurin hutun garkuna, domin mutanena da suke nemana.

  5. A can zan mayar mata da gonakin inabinta, zan kuma sa Kwarin Akor yă zama ƙofar bege. A can za tă rera kamar a kwanakin ƙuruciyarta, kamar a lokacin da ta fita daga Masar.