Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Discipline

25 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka tashi! Me kake yi kwance rubda ciki?

  2. Isra’ilawa sun yi zunubi, sun karya sharaɗin da na yi musu. Sun ɗauki waɗansu abubuwan da aka keɓe; sun yi sata, sun yi ƙarya, sun ɓoye su cikin kayansu.

  3. Shi ne ya sa Isra’ilawa suka kāsa yin tsayayya da abokan gābansu; suka juya suka gudu domin za a hallaka su. Ba zan sāke kasancewa tare da ku ba sai in kun hallaka duk abin da aka keɓe don hallaka.

  4. “Tashi, ka je ka tsarkake mutane. Ka ce musu su tsarkake kansu, su yi shiri domin gobe; gama ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, a cikinku akwai abubuwan da aka keɓe, ya Isra’ilawa. Ba za ku iya yin tsayayya da abokan gābanku ba sai in kun rabu da abubuwan nan da aka haramta.

  5. “ ‘Da safe ku zo kabila-kabila. Kabilar da Ubangiji ya ware, za tă zo gaba gida-gida; gidan da Ubangiji ya ware, za su zo gaba iyali-iyali. Iyalin kuma da Ubangiji ya ware, za su zo gaba mutum bayan mutum.

  6. Mutumin da aka same shi da haramtattun abubuwan kuwa za a ƙone shi, duk da mallakarsa domin ya karya sharaɗin da Ubangiji ya yi muku, ya yi abin kunya a Isra’ila!’ ”

  7. Kashegari da sassafe Yoshuwa ya sa Isra’ilawa suka fito kabila-kabila, aka ware kabilar Yahuda.

  8. Gidan Yahuda suka zo gaba, sai aka ware gidan Zera, aka sa suka fito iyali-iyali, sai aka ware Zabdi.

  9. Yoshuwa kuwa ya sa iyalin Zabdi suka fito mutum-mutum, sai kuwa aka ware Akan ɗan Karmi, ɗan Zimri, ɗan Zera na kabilar Yahuda.

  10. Sai Yoshuwa ya ce wa Akan, “Ɗana, sai ka ba Ubangiji, Allah na Isra’ila ɗaukaka, ka yi masa yabo. Ka gaya mini abin da ka yi; kada ka ɓoye mini.”

  11. Akan kuwa ya amsa ya ce, “Gaskiya ne! Na yi wa Ubangiji, Allah na Isra’ila zunubi. Ga abin da na yi.

  12. A cikin ganimar, na ga doguwar riga mai kyau irin ta Babilon, da shekel ɗari biyu na azurfa, da kuma sandan zinariya mai nauyin shekel hamsin, sai raina ya so su, na kuwa kwashe su. Na tona rami a cikin ƙasa a tentina; na ɓoye.”

  13. Sai Yoshuwa ya aiki ’yan aika suka tafi da gudu zuwa tenti ɗin, haka kuwa suka same su a ɓoye a tentinsa, da azurfa a ƙarƙashi.

  14. Suka kwashe kayan daga tenti ɗin suka kawo wa Yoshuwa da sauran Isra’ilawa, suka baza su a gaban Ubangiji.

  15. Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka ɗauki Akan ɗan Zera, da azurfar, doguwar rigar, sandan zinariya, ’ya’yansa maza da mata, shanunsa, jakuna da tumaki, tentinsa da duk abin da yake da shi, suka kai su Kwarin Akor.

  16. Yoshuwa ya ce, “Me ya sa ka jawo mana wahala haka? Ubangiji zai kawo maka wahala kai ma a yau.” Sai dukan Isra’ilawa suka jajjefe shi, bayan da suka gama jifarsa sai suka ƙone sauran.

  17. Suka tara manyan duwatsu a kan Akan, tarin duwatsun na nan a can har wa yau. Sa’an nan Ubangiji ya huce daga fushinsa mai zafi. Saboda haka ake kiran wurin Kwarin Akor.

  18. Sa’an nan Isra’ilawa suka ce, “Wace kabila ce cikin kabilan Isra’ila ba tă zo taro a gaban Ubangiji ba?” Gama an yi rantsuwa cewa duk wanda ya kāsa zuwa taro a gaban Ubangiji a Mizfa lalle a kashe shi.

  19. To, Isra’ilawa suka yi juyayin ’yan’uwansu, mutanen Benyamin. “Yau an hallaka kabila daga cikin Isra’ila.

  20. Yaya za mu ba wa waɗanda suka rage mata, da yake mun riga mun yi rantsuwa a gaban Ubangiji, ba za mu ba su ɗaya daga ’ya’yanmu su aura ba?”

  21. Sa’an nan suka ce, “Wace kabila ce cikin kabilan Isra’ila ba tă zo taro a gaban Ubangiji a Mizfa ba?” Sai su gane cewa babu wani daga Yabesh Gileyad da ya zo sansani don taron.

  22. Gama da aka yi ƙidaya mutane, sai aka gane cewa babu wani daga mutanen Yabesh Gileyad da yake a can.

  23. Saboda haka sai taron ya umarci jarumai dubu goma sha biyu su je Yabesh Gileyad su karkashe waɗanda suke zaune a can, duk da mata da yara.

  24. Suka ce musu, “Ga abin da za ku yi. Ku karkashe duk namiji da kowace macen da ta riga ta san namiji.”

  25. Suka samu a cikin mutanen da suke zaune a Yabesh Gileyad mata ɗari huɗu da ba su taɓa kwana da namiji ba, suka kwashe su zuwa sansani a Shilo a Kan’ana.