Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Ox

111 ayoyi · 73 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bijimai masu yawa sun kewaye ni; bijimai masu ƙarfi na Bashan sun sa ni a tsaka.

  2. Ba na bukatan bijimi daga turkenku ko awaki daga garkunanku,

  3. Ka tsawata wa naman jejin nan a cikin kyauro, garken bijimai a cikin ’yan maruƙan al’ummai. Ka ƙasƙantar, bari yă kawo sandunan azurfa. Ka watsar da al’ummai waɗanda suke jin daɗin yaƙi.

  4. Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya, fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.

  5. Suka sauke Ɗaukakarsu saboda siffar bijimi, wanda yake cin ciyawa.

  6. shanunmu za su ja kaya masu nauyi. Ba za a sami tashin hankali a katangarmu ba, ba zuwan zaman bauta, ba jin kukan damuwa a titunanmu.

  7. Nan take, ya bi ta kamar saniyar da za a kai mayanka, kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo

  8. Ta shirya abincinta gauraye da ruwan inabinta; ta kuma shirya teburinta.

  9. Inda ba shanu, wurin sa wa dabbobi abinci zai kasance ba kome, amma daga ƙarfin saniya ce yalwar girbi kan fito.

  10. Gara a ci abincin kayan ganye inda akwai ƙauna da a ci kiwotaccen saniya inda ƙiyayya take.

  11. Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka;

  12. Saniya ta san maigidanta, jaki ya san wurin sa wa dabbobi abinci maigidansa, amma Isra’ila ba su sani, mutanena ba su gane ba.”

  13. Game da dukan tuddai da dā ake nome da garemani kuwa, ba za ku ƙara je wurin ba saboda tsoron ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya; za su zama wuraren da ake kai shanu a sake su su yi ta yawo da kansu, tumaki kuma su yi ta gudu.

  14. Saniya da beyar za su yi kiwo tare, ƙananansu za su kwanta tare, zaki kuma zai ci ciyawa kamar saniya.

  15. Zuciyata ta yi kuka a kan Mowab; mutanenta sun gudu har zuwa Zowar, har zuwa Eglat Shelishiya. Sun haura zuwa Luhit, suna tafe suna kuka; a kan hanyar zuwa Horonayim suna makoki saboda hallakawarsu.

  16. Shanunku da jakunanku da suke huɗar gonakinku za su ci harawa mafi kyau, wanda an sheƙe shi da babban cokali mai yatsu da kuma babban cokali.

  17. zai zama muku da albarka, ku da kuke shuki iri kusa da kowane rafi, kuna kuma barin lafiyayyiyar makiyaya domin shanu da jakunanku.

  18. ’Ya’yanki sun sume; sun kwanta kusurwar kowane titi, kamar barewar da aka kama da tarko. Sun cika da fushin Ubangiji da kuma tsawatawar Allahnki.

  19. Sharon zai zama wurin kiwo don shanu, Kwarin Akor kuma wurin hutun garkuna, domin mutanena da suke nemana.

  20. Na kasance kamar ɗan rago marar faɗa wanda aka kai mayanka; ban gane cewa sun ƙulla mini maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da ’ya’yansa; bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.”

  21. “Tabbatacce na ji gurnanin Efraim yana cewa, ‘Ka hore ni kamar ɗan maraƙi mai ƙin ji, na kuwa horu. Ka mayar da ni, zan kuwa dawo, domin kai ne Ubangiji Allahna.

  22. “Masar kyakkyawar karsana ce, amma bobuwa tana zuwa a kanta daga arewa.

  23. Sojojin da ta yi hayarsu a cikinta suna kamar ’yan maruƙa masu kitse. Su ma za su juya su kuma gudu gaba ɗaya, ba za su iya tsayawa ba, gama ranar masifa tana zuwa a kansu, lokacin da za su sha hukunci.

  24. “Muryar kukansu na tashi daga Heshbon zuwa Eleyale da Yahaz, daga Zowar har zuwa Horonayim da Eglat Shelishiya, gama har ruwan Nimrim ma sun bushe.

  25. “Saboda kuna farin ciki kuna kuma murna, ku da kuka washe gādona, domin kuna tsalle kamar karsana mai sussuka hatsi kuna kuma haniniya kamar ingarmu.