Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Salvation

158 ayoyi · 106 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka.

  2. Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!”

  3. In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga ayyuka ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.

  4. Har yanzu ina da tambaya. Sun yi tuntuɓe har ya kai ga fāɗuwar da ba za su iya tashi ba ne? Sam, ko kaɗan! A maimako, saboda laifinsu ne ceto ya zo ga Al’ummai don a sa mutanen Isra’ila su ji kishi.

  5. da fata zan rura kabilata a ta kowace hanya su ji kishi har ma yă sa in ceci waɗansunsu.

  6. Ta haka kuwa za a ceci dukan Isra’ila, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai ceto zai zo daga Sihiyona; zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub.

  7. Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya.

  8. Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne.

  9. Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara.

  10. Saboda haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Duk wanda yake taƙama, ya yi taƙama a cikin Ubangiji.”

  11. Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu.

  12. Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  13. Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka.

  14. Gama ya ce, “A lokacin samun alherina, na ji ka, a ranar samun ceto kuma, na taimake ka.” Ina gaya muku, yanzu ne lokacin samun alherin Allah, yanzu ne ranar samun ceto.

  15. Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa.

  16. Shi wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu don yă cece mu daga wannan mugun zamani na yanzu, bisa ga nufin Allah wanda yake kuma Ubanmu,

  17. Kada in taɓa yin taƙama ga kome sai dai a cikin gicciyen Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa aka gicciye duniya a gare ni, aka kuma gicciye ni ga duniya.

  18. An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki.

  19. ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku.

  20. Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah.

  21. Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai.

  22. Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa.

  23. Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.

  24. ba tare da kun ji tsoron waɗanda suke gāba da ku ta kowace hanya ba. Wannan alama ce a gare su cewa za a hallaka su, amma a gare ku za a cece ku, wannan tabbacin kuwa daga wurin Allah ne.

  25. Gama an ba ku zarafi a madadin Kiristi cewa ba gaskatawa da shi kaɗai ba kuka yi ba, har ma ku sha wahala dominsa,