Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Salvation

158 ayoyi · 106 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zan kuma sa ƙiyayya tsakaninka da macen, tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ragargaje kanka, kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”

  2. “Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.

  3. Suka kama hanya daga Dutsen Hor ta hanya zuwa Jan Teku, don su kauce wa Edom. Amma mutane suka rasa haƙuri a hanya;

  4. suka yi wa Allah da Musa gunaguni, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu mu mutu a wannan hamada? Babu abinci! Babu ruwa! Mu dai mun gaji da wannan abinci marar amfani!”

  5. Sai Ubangiji ya aiko da macizai masu dafin a cikinsu, suka sassari mutane, Isra’ilawa masu yawa kuwa suka mutu.

  6. Mutanen suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi, da muka yi wa Ubangiji da kai gunaguni. Ka yi addu’a don Ubangiji yă ɗauke mana macizan nan.” Saboda haka Musa ya yi addu’a domin mutane.

  7. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera siffar maciji ka rataye shi a bisa doguwar sanda; kowa da maciji ya sare shi, idan ya dubi macijin nan da ka rataye, zai rayu.”

  8. Saboda haka Musa ya ƙera macijin tagulla, ya kuma rataye shi bisa doguwar sanda. Sa’an nan duk wanda maciji ya sare shi, ya kuma dubi macijin tagullar, zai warke.

  9. Yeshurun ya yi ƙiba, ya yi kauri; cike da abinci, ya zama da nauyi, ya kuma zama sumul. Ya yashe Allahn da ya yi shi, ya ƙi Dutse Cetonsa.

  10. Ka ba ni garkuwar nasararka; ka sauko don ka sa in sami girma.

  11. “Ubangiji yana a raye! Yabo ta tabbata ga Dutsena! Ɗaukaka ga Allah, Dutse, Mai Cetona!

  12. “Ya ba wa sarkinsa kyakkyawan nasara; ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”

  13. Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka; ku yi shelar cetonsa kowace rana.

  14. “Yanzu ka tashi, ya Ubangiji Allah, ka zo wurin hutunka,

  15. Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela

  16. Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni; ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka.

  17. don in furta yabanka cikin ƙofofin ’Yar Sihiyona a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka.

  18. Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona; Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka. Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata.

  19. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka. Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi!

  20. ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini, gama kai ne Allah Mai cetona, kuma begena yana a kanka dukan yini.

  21. Ka ɗaga māshi da kuma abin da ake jefa a kan waɗanda suke fafarata. Ka ce wa raina, “Ni ne cetonka.”

  22. Ceton adalai kan zo daga Ubangiji; shi ne mafaka a lokacin wahala.

  23. Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata; ina maganar amincinka da cetonka. Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka a gaban taron jama’arka mai girma ba.

  24. Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “Ubangiji mai girma ne!”

  25. Ka mayar mini farin cikin cetonka ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni.