Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Salvation: Is of love
Ayoyi game da Is of love
Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.
Ga yadda Allah ya nuna ƙaunarsa a cikinmu, Allah ya aiki makaɗaici Ɗansa zuwa duniya domin mu rayu ta wurinsa.
Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yă zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu.