Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Agriculture or Husbandry

132 ayoyi · 75 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi.

  2. Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’ “Za a la’anta ƙasa saboda kai. Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.

  3. Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za ka kuwa ci ganyayen gona.

  4. Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa, da yake daga cikinta aka yi ka. Gama kai turɓaya ne, kuma ga turɓaya za ka koma.”

  5. Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi.

  6. Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi.

  7. Ya ba shi suna Nuhu ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.”

  8. Nuhu, mutumin ƙasa, shi ne farko da ya fara yin gonar inabi.

  9. Lot ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, sai ya ga kwarin yana da ciyawa mai kyau ƙwarai sai ka ce lambun Ubangiji, kamar ƙasar Masar, wajajen Zowar. (Wannan fa kafin Ubangiji yă hallaka Sodom da Gomorra.)

  10. Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.”

  11. “In mutum ya sa dabbobinsa su yi kiwo a fili ko a gonar inabi, ya kuma bar dabbobinsa suka yi ɓarna a cikin gonar wani, sai a sa mai dabbar yă biya tara daga amfanin gonarsa mafi kyau duka.

  12. “In gobara ta tashi, ta kuma bazu cikin ƙayayyuwa, har ta cinye tarin hatsi, ko hatsin da ke tsaye, ko dukan gonar, dole wanda ya sa wutar, yă biya taran da aka yanka masa saboda ɓarnan da wutar ta yi.

  13. “In kun ba wa jama’ata matalauta da suke tsakaninku bashin kuɗi, kada ku zama kamar masu ba da rance; kada ku sa yă biya da ruwa.

  14. “Shekara shida za ku nome gonakinku ku girbe amfanin gonar,

  15. amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun.

  16. Yaya wani zai sani ko ka ji daɗina da kuma mutanenka, in ba ka tafi tare da mu ba? Mene ne kuma zai bambanta ni da mutanenka daga sauran jama’ar da suke a duniya?”

  17. “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku.

  18. Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu.

  19. “ ‘Kada a sayar da gona ɗinɗinɗin, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi ne kawai, kuma ’yan haya nawa.

  20. Ko’ina a ƙasar da kuke da mallaka, dole ku tanadar da dama fansar ƙasar.

  21. “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta, ya kuma sayar da mallakarsa, sai danginsa na kusa yă je yă fanshi abin da mutumin ƙasarsa ya sayar.

  22. In mutumin ba shi da wanda zai fansa masa ita, shi kansa kuwa ya wadace, ya kuma sami isashen halin fansarta,

  23. sai yă lasafta yawan shekarun da aka yi tun da an sayar da filin. Kuɗin filin zai dangana ga yawan shekarun da suka rage kafin shekara hamsin ta murna da za tă zo; sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.

  24. Amma in bai sami halin sāke biyansa ba, abin nan da ya sayar zai ci gaba da zama mallakar mai sayan, sai Shekara ta Murna. Za a maido masa da ita a Shekara ta Murna, sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.

  25. zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu.