Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Agriculture or Husbandry: Diligence

6 ayoyi · 75 fannoni

Ayoyi game da Diligence

  1. Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka;

  2. domin dukiya ba ta dawwama har abada, ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara.

  3. Sa’ad da aka yanki ingirci sabon toho kuma ya bayyana aka kuma tattara ciyawa daga tuddai,

  4. gashin raguna za su tanada maka tufafi, za ka iya sayi gonaki masu kyau da kuɗin awaki.

  5. Za ka kasance da madarar awaki mai yawa don ka ciyar da kanka da kuma iyalinka ka kuma inganta bayinka mata.

  6. Ka shuka irinka da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka.