Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Agriculture or Husbandry: The promises of God's blessings on
Ayoyi game da The promises of God's blessings on
zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu.
Zai ƙaunace ku, yă albarkace ku, yă kuma ƙara yawanku. Zai albarkaci ’ya’yanku, amfanin gonarku; hatsinku, sabon ruwan inabinku da kuma mai, ƙanana shanunku, da ’yan tumaki na tumakinku, a ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku.
sai in aika da ruwan sama a ƙasarku a lokacinsa, ruwan saman bazara da kuma na kaka, don ku tattara hatsinku, sabon inabinku da kuma manku.
Zan tanadar da ciyawa a filaye don shanunku, za ku ci, ku kuma ƙoshi.