Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Agriculture or Husbandry: Produce of, often blasted because of sin

5 ayoyi · 75 fannoni

Ayoyi game da Produce of, often blasted because of sin

  1. Kadada goma na gonar inabi zai ba da garwan ruwan inabi ɗaya kaɗai, mudu guda na iri kuma zai ba da efa na hatsi guda kurum.”

  2. A wannan rana, a kowane wuri inda akwai kuringa dubu da kuɗinsu ya kai shekel dubu na azurfa, ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne kawai za su kasance a can.

  3. Za su shuka alkama, su girbe ƙayayyuwa; za su gajiyar da kansu, ba za su kuwa sami kome ba. Saboda haka ku sha kunyar abin da kuka girbe saboda zafin fushin Ubangiji.”

  4. Filaye sun zama marasa amfani, ƙasa ta bushe; an lalatar da hatsi, sabon ruwan inabin ya bushe, mai kuma ba amfani.

  5. Ku fid da zuciya, ku manoma, ku yi ihu, ku masu noma inabi; ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir, saboda an lalata girbin filaye.