Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Agriculture or Husbandry: Soil of Canaan suited to

4 ayoyi · 75 fannoni

Ayoyi game da Soil of Canaan suited to

  1. Lot ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, sai ya ga kwarin yana da ciyawa mai kyau ƙwarai sai ka ce lambun Ubangiji, kamar ƙasar Masar, wajajen Zowar. (Wannan fa kafin Ubangiji yă hallaka Sodom da Gomorra.)

  2. Gama Ubangiji Allahnku yana fitar da ku zuwa cikin ƙasa mai kyau, ƙasa mai rafuffuka da tafkunan ruwa, tare da maɓulɓulai masu gudu a kwari da tuddai;

  3. ƙasa mai alkama da sha’ir, inabi da ɓaure, rumman, man zaitun da zuma;

  4. ƙasa inda abinci ba zai yi ƙaranci ba, ba kuma za ku rasa kome ba; ƙasa ce inda ƙarfe ne duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta.