Skip to content

Boaz

24 ayoyi · 4 'yan gida

An kuma san shi da: Booz

Ayoyin da suka ambaci Boaz

  1. To, fa, Na’omi tana da dangi a gefen mijinta da iyalin Elimelek, mutum mai martaba, mai suna Bowaz.

  2. Saboda haka ta tafi ta fara kala a gonaki a bayan masu girbi. Sai ya zamana, ta sami kanta tana aiki a gonar da take ta Bowaz, wanda yake daga dangin Elimelek.

  3. Sai ga Bowaz ya iso daga Betlehem ya gai da masu girbi, “Ubangiji yă kasance tare da ku!” Sai suka amsa, “Ubangiji yă albarkace ka!”

  4. Sai Bowaz ya tambayi shugaban masu girbinsa, “Wace yarinya ce wannan?”

  5. Saboda haka Bowaz ya ce wa Rut, “’Yata, ki saurare ni. Kada ki tafi ki yi kala a wani gona, kada kuma ki tafi daga nan. Ki tsaya nan tare da ’yan matana bayi.

  6. Bowaz ya amsa, “An faɗa mini duka game da abin kika yi domin surukarki tun mutuwar mijinki, yadda kika bar mahaifinki da mahaifiyarki da kuma ƙasarki kika zo ki yi zama da mutanen da ba ki taɓa sani ba.

  7. A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.” Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa.

  8. Da ta tashi don tă yi kala, sai Bowaz ya yi umarni wa samarinsa cewa, “Ko ta tara daga cikin dammuna, kada ku wulaƙanta ta.

  9. Surukarta ta tambaye ta, “Ina kika yi kala a yau? Ina kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga mutumin nan ta ya lura da ke!” Sai Rut ta faɗa wa surukarta game da wurin wanda ta yi ta aiki. Ta ce, “Sunan mutumin da na yi aiki da shi a yau Bowaz ne.”

  10. Saboda haka Rut ta tsaya kusa da bayi mata na Bowaz don tă yi kala sai da girbin sha’ir da na alkama suka ƙare. Ta kuwa zauna tare da surukarta.

  11. Bowaz wanda kike aiki da bayinsa ’yan mata ba danginmu ne na kusa ba? Da daren yau zai sussuka sha’ir nasa a masussuka.

  12. Sa’ad da Bowaz ya gama ci da sha yana kuma cikin farin ciki, sai ya tafi ya kwanta a ƙarshen tarin hatsi. Rut kuwa ta sulalle ta je ta buɗe ƙafafunsa ta kwanta.

  13. Ana cikin haka Bowaz ya haura zuwa ƙofar gari ya tafi ya zauna a can. Sa’ad da dangi mai fansan da ya yi zance ya iso, Bowaz ya ce, “Zo nan abokina ka zauna.” Saboda haka ya ratso ya zauna.

  14. Sa’an nan Bowaz ya ce, “A ranar da ka saya filin daga Na’omi da kuma daga Rut mutuniyar Mowab, ka sayi gwauruwar marigayin nan, domin ka riƙe sunan marigayin da kuma kayansa.”

  15. Saboda haka dangin nan mai fansa ya ce wa Bowaz, “Saye shi wa kanka.” Sai ya cire takalminsa.

  16. Sa’an nan Bowaz ya yi shela wa dattawa da kuma dukan mutane, “A yau ku ne shaidu cewa na saya daga Na’omi dukan mallakar Elimelek, Kiliyon da kuma Malon.

  17. Sai Bowaz ya ɗauki Rut ta kuwa zama matarsa. Sa’an nan ya kwana da ita, Ubangiji kuma ya sa ta yi ciki, ta haifi ɗa.

  18. Salmon ya haifi Bowaz, Bowaz ya haifi Obed,

  19. Ya ta da ginshiƙai a shirayin haikali. Ya ba wa ginshiƙi na wajen kudu sunan Yakin, na wajen arewa kuma ya kira Bowaz.

  20. Nashon shi ne mahaifin Salma, Salma shi ne mahaifin Bowaz,

  21. Bowaz shi ne mahaifin Obed kuma Obed shi ne mahaifin Yesse.

  22. Ya kafa ginshiƙan a gaban haikalin, ɗaya a kudu, ɗaya kuma a arewa. Ya kira wanda yake kudun, Yakin, na arewan kuwa ya kira Bowaz.

  23. Salmon ya haifi Bowaz, wanda Rahab ce mahaifiyarsa, Bowaz ya haifi Obed, wanda Rut ce mahaifiyarsa, Obed ya haifi Yesse,

  24. ɗan Yesse, ɗan Obed, ɗan Bowaz, ɗan Salmon, ɗan Nashon,