Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reaping

44 ayoyi · 25 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.”

  2. “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku.

  3. “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, kuka kuma girbe amfanin gonarta, sai ku kawo wa firist damin hatsi na farko da kuka girbe.

  4. “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin gonarku, kada ku girbe har ƙarshen gefen gonar, ko ku yi kalar girbinku. Ku bar su wa matalauta da baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”

  5. Kada ku girbe abin da ya yi girma ba tare da ku kuka shuka ba, ko ku girbe inabin da ba ku aske ba. Ƙasar za tă kasance da shekarar hutu.

  6. Shekara ta hamsin za tă zama ta murna a gare ku; kada ku yi shuki, kada kuma ku yi girbi abin da ya yi girma da kansa, ko ku girbe inabin da ba ku lura da shi ba.

  7. Ku ƙirga makoni bakwai, wato, ku fara ƙirga mako bakwai ɗin daga lokacin da kuka sa lauje don ku yanke hatsinku da suke tsaye.

  8. In kun shiga gonar hatsin maƙwabcinku, za ku iya murmure tsabar da hannuwanku, amma kada ku sa lauje ku yanka hatsinsa da yake tsaye.

  9. Sai ga Bowaz ya iso daga Betlehem ya gai da masu girbi, “Ubangiji yă kasance tare da ku!” Sai suka amsa, “Ubangiji yă albarkace ka!”

  10. Sai Bowaz ya tambayi shugaban masu girbinsa, “Wace yarinya ce wannan?”

  11. Shugaban ya amsa, “Ita ce mutuniyar Mowab da ta zo daga Mowab tare da Na’omi.

  12. Saboda haka Bowaz ya ce wa Rut, “’Yata, ki saurare ni. Kada ki tafi ki yi kala a wani gona, kada kuma ki tafi daga nan. Ki tsaya nan tare da ’yan matana bayi.

  13. Ki lura da gonar da mutanena suke girbi, ki bi su tare da ’yan matana. Na riga na faɗa wa mazan kada su taɓa ke. Kuma duk sa’ad da kika ji ƙishirwa, ki tafi ki ɗebo ruwa daga tulunan da mazan suka cika.”

  14. A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.” Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa.

  15. A lokacin kuwa mutanen Bet-Shemesh suna girbin alkamansu a kwari da suka ɗaga ido suka hangi akwatin alkawarin Ubangiji, sai suka yi farin ciki ganinsa.

  16. Yaron ya yi girma, wata rana sai ya tafi wurin mahaifinsa, wanda yake tare da masu girbi.

  17. Na kula cewa waɗanda suke huɗa gonar mugunta, da waɗanda suke shuka mugunta, su ne suke girbe mugunta.

  18. Suna girbi a gonakin da ba nasu ba, suna yin kala a gonar inabi ta mugaye.

  19. Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.

  20. Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.

  21. da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.

  22. Duk wanda ya shuka mugunta yakan girbe wahala, za a kuma hallaka sandar fushinsa.

  23. Zai zama kamar sa’ad da mai girbi ya tara hatsin da yake tsaye ya kuma girbe hatsin da hannunsa kamar sa’ad da mutum ya yi kala kawunan hatsi a Kwarin Refayim.

  24. Za su shuka alkama, su girbe ƙayayyuwa; za su gajiyar da kansu, ba za su kuwa sami kome ba. Saboda haka ku sha kunyar abin da kuka girbe saboda zafin fushin Ubangiji.”

  25. “Gama sun shuka iska don haka za su girbe guguwa. Hatsin da yake tsaye ba shi da kai, ba zai yi tsaba ba. Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci.