Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reaping

44 ayoyi · 25 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku shuka wa kanku adalci, ku girbe ’ya’yan jinƙai marar ƙarewa, ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba; gama lokaci ne na neman Ubangiji, sai ya zo ya zubo adalci a kanku.

  2. Amma kun shuka mugunta, kuka girbe mugu kuka ci ’ya’yan ruɗu. Domin kun dogara da ƙarfinku da kuma a jarumawanku masu yawa,

  3. Za ku yi shuki amma ba za ku girba ba; za ku matse zaitun amma ba za ku yi amfani da mai wa kanku ba, za ku tattaka ’ya’yan inabi amma ba za ku sha ruwan inabin ba.

  4. Ku ƙyale su su yi girma tare sai lokacin girbi. A lokacin zan gaya wa masu girbi, da fari ku tara ciyayin ku kuma daure su dami-dami don a ƙone; sa’an nan ku tara alkamar ku kuma kawo su cikin rumbuna.’ ”

  5. abokin gāban da yake shuka su kuwa, Iblis ne. Lokacin girbi kuma shi ne ƙarshen zamani, masu girbin kuwa su ne mala’iku.

  6. “Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani.

  7. Ɗan Mutum zai aiki mala’ikunsa, su kuwa cire daga mulkinsa kome da yake jawo zunubi da kuma duk masu aikata mugunta.

  8. Za su jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.

  9. Sa’an nan masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”

  10. Da ƙwayan ya nuna, sai yă sa lauje yă yanka, domin lokacin girbi ya yi.”

  11. Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.

  12. Na aike ku girbin abin da ba ku yi aikinsa ba. Waɗansu sun yi aikin nan mai wahala, ku kuwa kun sami ladan aikinsu.”

  13. In muka shuka iri na ruhaniya a cikinku, ashe, bai kamata mu yi girbin abin biyan bukatarmu daga gare ku ba?

  14. Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami.

  15. Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba.

  16. Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki.

  17. Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani da ya yi kamar “ɗan mutum” tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa.

  18. Sai wani mala’ika ya fito daga haikali ya kuma yi kira da babbar murya ga wannan mai zaune a kan girgijen ya ce, “Ɗauki laujenka ka yi girbi, domin lokacin girbi ya yi, gama amfanin da yake duniya ya nuna.”

  19. Sai wannan mai zaune a girgijen ya wurga laujensa a duniya, sai aka kuwa girbe duniya.