Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Obed

14 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Matan da suke zama a wurin suka ce, “Na’omi ta sami yaro.” Suka kuwa ba shi suna Obed. Shi ne ya haifi Yesse, mahaifin Dawuda.

  2. Ga asalin zuriyar Ferez. Ferez shi ne mahaifin Hezron,

  3. Hezron ya haifi Ram, Ram ya haifi Amminadab,

  4. Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,

  5. Salmon ya haifi Bowaz, Bowaz ya haifi Obed,

  6. Obed ya haifi Yesse, Yesse kuwa ya haifi Dawuda.

  7. Bowaz shi ne mahaifin Obed kuma Obed shi ne mahaifin Yesse.

  8. Zabad shi ne mahaifin Eflal, Eflal shi ne mahaifin Obed,

  9. Obed shi ne mahaifin Yehu, Yehu shi ne mahaifin Azariya,

  10. Eliyel, Obed da Ya’asiyel mutumin Mezob.

  11. ’Ya’yan Shemahiya maza su ne, Otni, Rafayel, Obed da Elzabad; danginsa Elihu da Shemahiya su ma jarumawa ne.

  12. A shekara ta bakwai Yehohiyada ya nuna ƙarfinsa. Ya yi alkawari da shugabanni na ɗari-ɗari, Azariya ɗan Yeroham, Ishmayel ɗan Yehohanan, Azariya ɗan Obed, Ma’asehiya ɗan Adahiya, da Elishafat ɗan Zikri.

  13. Salmon ya haifi Bowaz, wanda Rahab ce mahaifiyarsa, Bowaz ya haifi Obed, wanda Rut ce mahaifiyarsa, Obed ya haifi Yesse,

  14. ɗan Yesse, ɗan Obed, ɗan Bowaz, ɗan Salmon, ɗan Nashon,