Skip to content

Hezron

13 ayoyi · 9 'yan gida

An kuma san shi da: Esrom

Ayoyin da suka ambaci Hezron

  1. ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan, Shela, Ferez da Zera (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan’ana). ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.

  2. Zuriyar Ferez kuwa, daga Hezron, kabilar Hezronawa; daga Hamul; kabilar Hamulawa.

  3. Ga asalin zuriyar Ferez. Ferez shi ne mahaifin Hezron,

  4. Hezron ya haifi Ram, Ram ya haifi Amminadab,

  5. ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.

  6. ’Ya’ya maza da aka haifa wa Hezron su ne, Yerameyel, Ram da Kaleb.

  7. Kaleb ɗan Hezron ya haifi yara ta wurin matarsa Azuba (da kuma ta wurin Yeriyot). Waɗannan su ne ’ya’yan Azuba maza. Yesher, Shobab da Ardon.

  8. Daga baya, Hezron ya kwana da ’yar Makir mahaifin Gileyad (ya aure ta sa’ad da take da shekara sittin), ta haifa masa Segub.

  9. Bayan Hezron ya mutu a Kaleb Efrata, sai Abiya matar Hezron ta haifa masa Asshur mahaifin Tekowa.

  10. ’Ya’yan Yerameyel maza, ɗan farin Hezron su ne, Ram shi ne ɗan fari, sai Buna, Oren, Ozem da Ahiya.

  11. Zuriyoyin Yahuda su ne, Ferez, Hezron, Karmi, Hur da Shobal.

  12. Yahuda ya haifi Ferez da Zera, waɗanda Tamar ce mahaifiyarsu; Ferez ya haifi Hezron, Hezron ya haifi Ram,

  13. ɗan Amminadab, ɗan Ram, ɗan Hezron, ɗan Ferez, ɗan Yahuda,