Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pharez

11 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Amma sa’ad da ya janye hannunsa, sai ɗan’uwansa ya fito, sai ta ce, “Wato, haka ne ka keta ka fito!” Sai aka ba shi suna Ferez.

  2. ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan, Shela, Ferez da Zera (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan’ana). ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.

  3. Zuriyar Yahuda bisa ga kabilansu, daga Shela, kabilar Shelayawa daga Ferez, kabilar Ferezawa; daga Zera, kabilar Zerawa;

  4. Zuriyar Ferez kuwa, daga Hezron, kabilar Hezronawa; daga Hamul; kabilar Hamulawa.

  5. Tamar, surukar Yahuda, ta haifa masa Ferez da Zera. Yahuda ya haifi ’ya’ya maza biyar ne.

  6. ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.

  7. Uttai ɗan Ammihud, ɗan Omri, ɗan Imri, ɗan Bani, zuriyar Ferez ɗan Yahuda.

  8. yayinda sauran mutane daga Yahuda da Benyamin suka zauna a Urushalima). Daga zuriyar Yahuda akwai, Atahiya ɗan Uzziya, ɗan Zakariya, ɗan Amariya, ɗan Shefatiya, ɗan Mahalalel, wani zuriyar Ferez;

  9. Zuriyar Ferez waɗanda suka zauna a Urushalima sun kai ɗari huɗu da sittin da takwas, dukansu kuwa muhimman mutane ne.

  10. Yahuda ya haifi Ferez da Zera, waɗanda Tamar ce mahaifiyarsu; Ferez ya haifi Hezron, Hezron ya haifi Ram,

  11. ɗan Amminadab, ɗan Ram, ɗan Hezron, ɗan Ferez, ɗan Yahuda,