Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Segub

5 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. A lokaci Ahab ne, Hiyel mutumin Betel ya sāke gina Yeriko. Ya kafa tushensa a bakin ran ɗan farinsa Abiram, ya kuma kafa ƙofofinsa a bakin ran autansa Segub, bisa ga maganar Ubangiji da ya yi ta wurin Yoshuwa ɗan Nun.

  2. Tamar, surukar Yahuda, ta haifa masa Ferez da Zera. Yahuda ya haifi ’ya’ya maza biyar ne.

  3. ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.

  4. Daga baya, Hezron ya kwana da ’yar Makir mahaifin Gileyad (ya aure ta sa’ad da take da shekara sittin), ta haifa masa Segub.

  5. Segub shi ne mahaifin Yayir, wanda ya yi mulkin garuruwa uku a Gileyad.