Skip to content

Shaphat

4 ayoyi · 1 ɗan gida

Ayoyin da suka ambaci Shaphat

  1. Ka kuma shafe Yehu ɗan Nimshi yă zama sarkin Isra’ila, ka shafe Elisha ɗan Shafat daga Abel-Mehola yă gāje ka a matsayin annabi.

  2. Sai Iliya ya tafi daga can ya sami Elisha ɗan Shafat, yana noma da shanu goma sha biyu masu garman noma, shi kansa yana jan na goma sha biyun. Iliya ya tafi wurinsa ya jefa mayafinsa a kan Elisha.

  3. Amma Yehoshafat ya yi tambaya ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu nemi nufin Ubangiji ta wurinsa?” Wani hafsan sarkin Isra’ila ya amsa ya ce, “Ai, akwai Elisha ɗan Shafat, wanda dā ya yi wa Iliya hidima.”

  4. Ya ce, “Bari Allah yă yi mini hukunci mai tsanani har ma fiye da haka, idan ban cire kan Elisha ɗan Shafat yau ba!”