Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 31:16kusan 1452 K.H.

    Su ne waɗanda suka bi shawarar Bala’am suka kuma zama sanadin sa Isra’ilawa suka juya wa Ubangiji baya, har ya kawo abin da ya faru da Feyor, har annoba ya kashe dukan mutanen Ubangiji.

  2. Ƙidaya 31:17kusan 1452 K.H.

    Yanzu ku kashe dukan yara maza, ku kuma kashe kowace macen da ta yi lalata da namiji,

  3. Ƙidaya 31:18kusan 1452 K.H.

    amma ku bar kowace yarinyar da ba tă taɓa yin lalata da namiji ba.

  4. Ƙidaya 31:19kusan 1452 K.H.

    “Dukanku da kuka kashe mutum, ko kuka taɓa wani da aka kashe, dole ku kasance a bayan sansani har kwana bakwai. A rana ta uku da rana ta bakwai dole ku tsabtacce kanku da kuma bayinku.

  5. Ƙidaya 31:20kusan 1452 K.H.

    Ku tsarkake kowace taguwa da kuma kome da aka yi da fata, da gashin akuya, ko kuwa itace.”

  6. Ƙidaya 31:21kusan 1452 K.H.

    Sa’an nan Eleyazar firist, ya ce wa sojojin da suka je yaƙi, “Wannan ita ce ƙa’idar da Ubangiji ya ba wa Musa.

  7. Ƙidaya 31:22kusan 1452 K.H.

    Zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, kuza, darma

  8. Ƙidaya 31:23kusan 1452 K.H.

    da dukan abin da wuta ba ta iya ci, dole yă shiga wuta sa’an nan zai zama da tsabta. Amma dole a kuma tsarkake ta da ruwan tsarkakewa. Duk abin da wuta za tă iya ci, dole a shigar da ita a ruwan tsarkakewa.

  9. Ƙidaya 31:24kusan 1452 K.H.

    A rana ta bakwai za ku wanke tufafinku, sa’an nan za ku tsarkaka, bayan haka ku shigo sansani.”

  10. Ƙidaya 31:25kusan 1452 K.H.

    Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce,

  11. Ƙidaya 31:26kusan 1452 K.H.

    “Da kai da Eleyazar firist, da shugabannin jama’a, ku ƙidaya dukan mutane da dabbobin da aka ci da yaƙi.

  12. Ƙidaya 31:27kusan 1452 K.H.

    Ku kasa ganimar kashi biyu, ku ba sojojin da suka tafi yaƙi kashi ɗaya, kashi ɗaya kuma ku ba wa jama’a.

  13. Ƙidaya 31:28kusan 1452 K.H.

    Daga sojojin da suka je yaƙin kuwa, ka ware ganima wa Ubangiji, ka ɗauki ɗaya daga cikin mutum ɗari biyar, da shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, da tumaki ɗari biyar.

  14. Ƙidaya 31:29kusan 1452 K.H.

    Ka ɗauki wannan sashe daga rabin rabonsu ka ba wa Eleyazar firist, a matsayin sashe na Ubangiji.

  15. Ƙidaya 31:30kusan 1452 K.H.

    Daga cikin rabin rabon Isra’ilawa, ka zaɓi ɗaya daga kowane hamsin na mutane, shanu, jakuna, tumaki, awaki ko kuma sauran dabbobi. Ka ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji.”

  16. Ƙidaya 31:31kusan 1452 K.H.

    Saboda haka Musa da Eleyazar suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  17. Ƙidaya 31:32kusan 1452 K.H.

    Yawan ganimar da sojoji suka kawo ita ce tumaki 675,000

  18. Ƙidaya 31:33kusan 1452 K.H.

    shanu 72,000

  19. Ƙidaya 31:34kusan 1452 K.H.

    da jakuna 61,000.

  20. Ƙidaya 31:35kusan 1452 K.H.

    Akwai kuma mata 32,000 da ba su yi lalata ba da namiji ba.

  21. Ƙidaya 31:36kusan 1452 K.H.

    Kashin da aka ba sojoji waɗanda suka tafi yaƙi shi ne, tumaki 337,500,

  22. Ƙidaya 31:37kusan 1452 K.H.

    tumakin da aka ware wa Ubangiji kuwa 657 ne;

  23. Ƙidaya 31:38kusan 1452 K.H.

    shanu 36,000, shanun da aka ware wa Ubangiji kuwa 72 ne;

  24. Ƙidaya 31:39kusan 1452 K.H.

    jakuna 30,500, jakunan da aka ware wa Ubangiji kuwa 61 ne;

  25. Ƙidaya 31:40kusan 1452 K.H.

    mutane 16,000, mutanen da aka ware wa Ubangiji kuwa 32 ne.