- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Maimaitawar Shari’a 1:1kusan 1451 K.H.
Waɗannan su ne kalmomin da Musa ya yi wa dukan Isra’ila, a hamada gabas da Urdun, wato, Araba, ɗaura da Suf, tsakanin Faran da Tofel, Laban, Hazerot da Dizahab.
- Maimaitawar Shari’a 1:2kusan 1451 K.H.
(Yakan ɗauki kwana goma sha ɗaya daga Horeb zuwa Kadesh Barneya ta hanyar Dutsen Seyir.)
- Maimaitawar Shari’a 1:3kusan 1451 K.H.
A shekara ta arba’in, a rana ta fari ga wata na goma sha ɗaya, Musa ya yi shela ga Isra’ilawa game da dukan abin da Ubangiji ya umarta shi game da su.
- Maimaitawar Shari’a 1:4kusan 1451 K.H.
Wannan ya faru bayan ya ci Sihon sarkin Amoriyawa wanda ya yi mulki a Heshbon da yaƙi. A Edireyi kuma ya ci Og sarkin Bashan wanda ya yi mulki a Ashtarot da yaƙi.
- Maimaitawar Shari’a 1:5kusan 1451 K.H.
Gabas da iyakar Mowab, Musa ya fara bayyana wannan doka, yana cewa,
- Maimaitawar Shari’a 1:6kusan 1451 K.H.
Ubangiji Allahnmu ya faɗa mana a Horeb cewa, “Daɗewarku a wannan dutse ya isa haka.
- Maimaitawar Shari’a 1:7kusan 1451 K.H.
Ku tashi, ku ci gaba zuwa ƙasar tudun Amoriyawa; ku tafi wurin dukan maƙwabta a cikin Araba, a cikin duwatsu, a gindin yammancin tuddai, a Negeb da kuma a ta kwaruruka, da ƙasar Kan’aniyawa da kuma zuwa Lebanon, har zuwa babban kogi, wato, Yuferites.
- Maimaitawar Shari’a 1:8kusan 1451 K.H.
Duba na riga na ba ku wannan ƙasa. Ku shiga ku mallaki ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninku, ga Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub, da kuma ga zuriyarsu bayansu.”
- Maimaitawar Shari’a 1:9kusan 1451 K.H.
A wancan lokaci na faɗa muku cewa, “Ku kaya ne masu nauyi da ni kaɗai ba zan iya ɗauka ba.
- Maimaitawar Shari’a 1:10kusan 1451 K.H.
Ubangiji Allahnku ya ƙara yawanku har yau kuka zama da yawa kamar taurari a sarari.
- Maimaitawar Shari’a 1:11kusan 1451 K.H.
Bari Ubangiji, Allahn kakanninku yă ƙara yawanku sau dubu, yă kuma albarkace ku yadda ya yi alkawari!
- Maimaitawar Shari’a 1:12kusan 1451 K.H.
Amma yaya zan ɗauka dukan damuwoyinku da nawayarku da kuma faɗace-faɗacenku duka ni kaɗai?
- Maimaitawar Shari’a 1:13kusan 1451 K.H.
Ku zaɓi waɗansu masu hikima, masu ganewa, da kuma mutanen da ake girmama daga kowace kabilarku, zan kuma sa su a kanku.”
- Maimaitawar Shari’a 1:14kusan 1451 K.H.
Kuka amsa mini, kuka ce, “Abin da ka ce za ka yi, yana da kyau.”
- Maimaitawar Shari’a 1:15kusan 1451 K.H.
Saboda haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma’amala da jama’a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu-dubu, waɗansu a kan ɗari-ɗari, waɗansu a kan hamsin-hamsin, waɗansu kuma a kan goma-goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku.
- Maimaitawar Shari’a 1:16kusan 1451 K.H.
Na kuma umarci alƙalanku a wancan lokaci, na ce, “Ku yi adalci cikin shari’a tsakanin ’yan’uwanku, ko damuwar tana tsakanin ’yan’uwa Isra’ilawa ne, ko kuwa tsakanin Isra’ilawa da baƙin da suke zaune a cikinku.
- Maimaitawar Shari’a 1:17kusan 1451 K.H.
Kada ku nuna sonkai a cikin hukuncinku, ku saurari kowane ɓangare, babba da ƙarami, kada ku ji tsoron wani, gama hukunci na Allah ne. Ku kawo kowane batun da ya sha ƙarfinku, zan kuwa saurare shi.”
- Maimaitawar Shari’a 1:18kusan 1451 K.H.
A wancan lokacin kuwa na faɗa muku dukan abin da ya kamata ku yi.
- Maimaitawar Shari’a 1:19kusan 1451 K.H.
Sa’an nan, muka kama hanya daga Horeb muka ratsa wajen ƙasar tudun Amoriyawa ta dukan hamadarta mai fāɗi, da kuma mai bantsoron da kuka gani, muka kuma kai Kadesh Barneya yadda Ubangiji, Allahnmu ya umarce mu.
- Maimaitawar Shari’a 1:20kusan 1451 K.H.
Sai na ce muku, “Kun iso ƙasar tudun Amoriyawa, wadda Ubangiji, Allahnmu yake ba mu.
- Maimaitawar Shari’a 1:21kusan 1451 K.H.
Duba, Ubangiji Allahnku ya ba ku ƙasar. Ku haura ku mallake ta yadda Ubangiji Allahn kakanninku ya faɗa muku. Kada ku ji tsoro, kada ku fid da zuciya.”
- Maimaitawar Shari’a 1:22kusan 1451 K.H.
Sai dukanku kuka zo wurina kuka ce, “Bari mu aiki mutane su yi gaba su leƙi mana asirin ƙasar, su kuma kawo mana labari game da hanyar da za mu bi, da kuma biranen da za mu shiga.”
- Maimaitawar Shari’a 1:23kusan 1451 K.H.
Ra’ayin nan naku ya yi mini kyau, saboda haka na zaɓe ku goma sha biyu, mutum guda daga kowace kabila.
- Maimaitawar Shari’a 1:24kusan 1451 K.H.
Suka tafi, suka haura zuwa ƙasar tudu, suka kai Kwarin Eshkol, suka leƙo asirin ƙasar.
- Maimaitawar Shari’a 1:25kusan 1451 K.H.
Suka ɗebi ’ya’yan itatuwan ƙasar, suka sauko mana da su, suka kuma ba da labari cewa, “Ƙasar da Ubangiji Allahnmu yake ba mu, kyakkyawa ce.”