Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Offerings

433 ayoyi · 61 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji.

  2. Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo,

  3. Yaƙub kuwa ya kafa al’amudin dutse a inda Allah ya yi magana da shi, ya zuba hadaya ta sha a kansa; ya kuma zuba mai a kansa.

  4. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Zuciyar Fir’auna taurariya ce, ya ƙi yă bar mutanen su tafi.

  5. “Duk wanda ya yi hadaya ga wani allah ban da Ubangiji, dole a hallaka shi.

  6. “Kada ku jinkirta fitar da zakarku daga rumbunanku, ko harajin kayan da kuka saya. “Dole ku ba ni ’ya’yan farinku maza.

  7. Ku yi haka da shanunku da tumakinku. Bari su kasance da iyayensu mata, har kwana bakwai, amma ku ba ni su a rana ta takwas.

  8. “Ka ɗauki ɗayan ragon, sai Haruna da ’ya’yansa maza su ɗora hannuwansu a kansa.

  9. Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka shafa a bisa leɓen kunnen Haruna na dama, da bisa leɓen kunnuwan ’ya’yansa maza na dama, da kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden.

  10. Ka ɗibi jinin da yake a kan bagade, da man shafewa, ka yafa a kan Haruna da rigunansa, da kuma a kan ’ya’yansa maza da rigunansu. Sa’an nan shi da ’ya’yansa maza da rigunansu za su tsarkake.

  11. “Ka ɗebi kitse daga wannan rago, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebi kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake bisa hanta, da ƙoda biyu da kitsen da yake kansu, da cinyar dama. (Gama rago ne don naɗi.)

  12. Bayan haka, ka ɗauki ƙirjin ragon domin naɗin Haruna, ka kaɗa shi a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa. Wannan ƙirji zai zama rabonka.

  13. “Ka tsarkake ƙirji na hadaya ta kaɗawa, da cinya ta hadaya ta ɗagawa, waɗanda za a kaɗa a kuma ɗaga na ragon naɗin, wanda yake na Haruna da kuma na ’ya’yansa maza.

  14. Wannan zai zama rabon Haruna da ’ya’yansa maza daga Isra’ilawa. Gama wannan hadaya ta ɗagawa ce daga cikin hadayu na salama da Isra’ilawa za su miƙa wa Ubangiji.

  15. “Ka ɗauki ragon naɗi, ka dafa naman a tsattsarkan wuri.

  16. Haɗe da ɗan rago na farkon, ka miƙa mudun gari mai laushi wanda an gauraye da kwalaba ɗaya na tataccen mai zaitun, da kwalaba ɗaya na ruwan inabi don hadaya ta sha.

  17. Ka miƙa ɗaya ragon da yamma, tare da hadaya ta gari da hadaya ta sha kamar aka yi ta safe, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  18. Dole Haruna yă ƙone turare sa’ad da ya ƙuna fitilu da yamma, ta haka za a riƙa ƙona turare a gaban Ubangiji, daga tsara zuwa tsara.

  19. Ba za a ƙona wani irin turare dabam a bisa wannan bagade ba, ba kuma za a miƙa hadaya ta ƙonawa, ko ta hatsi, ko ta sha a bisansa ba.

  20. Kowannen da ya ƙetare zuwa wurin waɗanda aka riga aka ƙidaya, dole yă ba da rabin shekel, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda nauyinsa garwa ashirin ne. Wannan rabin shekel hadaya ce ga Ubangiji.

  21. Masu arziki ba za su bayar fiye da rabin shekel ba, talakawa kuma ba za su bayar ƙasa da haka ba, sa’ad da za ku yi hadaya ga Ubangiji don kafara rayukanku.

  22. Duk waɗanda suke da niyya, maza da mata, gaba ɗaya, suka kawo kayan ado na zinariya na kowane iri. ’Yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri-iri. Dukansu suka miƙa zinariyarsu a matsayin hadaya ga Ubangiji.

  23. “ ‘In hadaya ta ƙonawar daga shanu ne, sai yă miƙa namiji marar lahani. Dole yă kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă zama yardajje ga Ubangiji.

  24. Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya ta ƙonawar, za a kuwa karɓa a madadinsa don a yi kafara dominsa.

  25. Zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji, Haruna kuwa da ’ya’yansa maza firist, za su kawo jinin su kuma yafa shi a kan bagaden a kowane gefe a mashigin Tentin Sujada.