Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Game da Gad ya ce, “Mai albarka ne wanda ya fadada mazaunin Gad! Gad yana zama a can kamar zaki, yana yayyage a hannu da kai.

  2. Ya zaɓi ƙasa mafi kyau wa kansa; aka ajiye masa rabon shugaba. Sa’ad da shugabannin mutane suka taru, ya aikata adalcin Ubangiji da kuma hukuncinsa game da Isra’ila.”

  3. Game da Dan ya ce, “Dan ɗan zaki ne, yana tsalle daga Bashan.”

  4. Game da Naftali ya ce, “Naftali ƙosasshe ne da tagomashin Ubangiji, ya kuma cika albarkarsa; zai gāji gefen kudu zuwa tafki.”

  5. Game da Asher ya ce, “Mafi albarka na ’ya’yan, shi ne Asher; bari yă sami tagomashi daga ’yan’uwansa, bari kuma yă wanke ƙafafunsa a cikin mai.

  6. Madogaran ƙofofinka za su zama ƙarfe da tagulla, ƙarfinka kuma zai zama daidai da kwanakinka.

  7. “Babu wani kamar Allah na Yeshurun, wanda yake hawa a bisa sammai don yă taimake ka a kan gizagizai kuma a cikin darajarsa.

  8. Allah madawwami shi ne mafakarka, a ƙarƙashina kuma madawwamin hannuwa ne. Zai kore abokin gābanka a gabanka, yana cewa, ‘Ka hallaka shi!’

  9. Haka Isra’ila zai zauna lafiya shi kaɗai; zuriyar Yaƙub a tsare a ƙasar hatsi da sabon ruwan inabi, inda sammai za su zuba raɓa.

  10. Kai mai albarka ne, ya Isra’ila! Wane ne yake kamar ka, mutanen da Ubangiji ya ceta? Shi ne mafakarka da mai taimakonka da kuma takobinka mai ɗaukaka. Abokan gābanka za su zo neman jinƙai a gabanka, za ka kuwa tattake masujadansu.”

  11. Sai Musa ya hau Dutsen Nebo daga filayen Mowab, zuwa ƙwanƙolin Fisga, wanda yake ƙetare Yeriko. A can Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, daga Gileyad zuwa Dan,

  12. da ta dukan Naftali, da yankin Efraim da na Manasse, dukan ƙasar Yahuda har zuwa Bahar Rum,

  13. da Negeb da dukan yankin Kwarin Yeriko, Birnin Dabino, har zuwa Zowar.

  14. Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, “Wannan ce ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, sa’ad da na ce, ‘Zan ba da ita ga zuriyarku.’ Na bar ka ka gani da idanunka, amma ba za ka haye zuwa cikinta ba.”

  15. Nan fa, a ƙasar Mowab Musa bawan Ubangiji ya mutu, yadda Ubangiji ya faɗa.

  16. Aka binne shi a Mowab, a kwarin kusa da Bet-Feyor, amma har wa yau babu wanda ya san inda kabarinsa yake.

  17. Musa yana da shekara ɗari da ashirin sa’ad da ya mutu, duk da haka idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuwa bai ragu ba.

  18. Isra’ilawa suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab kwana talatin, sai da lokacin kuka, da na makoki suka ƙare.

  19. To, Yoshuwa ɗan Nun ya cika da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya hannuwansa a kansa. Saboda haka Isra’ilawa suka saurare shi, suka kuma aikata abin da Ubangiji ya umarci Musa.

  20. Tun daga nan ba a sāke yin wani annabi a Isra’ila kamar Musa ba, wanda Ubangiji ya san shi fuska da fuska,

  21. wanda kuma ya yi dukan waɗannan alamu banmamaki da al’ajaban da Ubangiji ya aike shi yă yi a Masar, da a kan Fir’auna, da a kan dukan shugabanninsa, da kuma a kan dukan ƙasarsa.

  22. Gama babu wani wanda ya taɓa nuna iko mai ƙarfi, ko yă aikata ayyukan banrazana waɗanda Musa ya yi a gaban dukan Isra’ila.