Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 30:7kusan 1452 K.H.

    mijinta kuwa ya ji game da wannan, amma bai ce mata kome ba, to, alkawarin da ta yi da kuma rantsuwar da ta yi, su tabbata.

  2. Ƙidaya 30:8kusan 1452 K.H.

    Amma in mijin ya hana ta sa’ad da ya ji, zai warware alkawari da kuma rantsuwar da ta yi da garaje, Ubangiji kuwa zai gafarce ta.

  3. Ƙidaya 30:9kusan 1452 K.H.

    “Duk wani alkawari ko rantsuwar da gwauruwa, ko macen da aurenta ya mutu, ta yi, zai tabbata a kanta.

  4. Ƙidaya 30:10kusan 1452 K.H.

    “In macen aure ta yi alkawari, ko ta rantse za tă yi wani abu,

  5. Ƙidaya 30:11kusan 1452 K.H.

    mijinta kuwa ya ji game da wannan, amma bai ce mata kome ba, bai kuma hana ta ba, to, dukan alkawari da kuma rantsuwar da ta yi su tabbata a kanta.

  6. Ƙidaya 30:12kusan 1452 K.H.

    Amma in mijin ya warware su sa’ad da ya ji, to, ba wani alkawari ko rantsuwar da ya fito daga leɓunanta da zai tabbata. Mijinta ya warware su, Ubangiji kuma zai gafarce ta.

  7. Ƙidaya 30:13kusan 1452 K.H.

    Mijinta yana iya tabbatar, ko yă rushe duk wani alkawari ko rantsuwar da ta ɗauka.

  8. Ƙidaya 30:14kusan 1452 K.H.

    Amma in mijinta bai ce mata kome ba, to, ya tabbatar da dukan alkawarinta da kuma rantsuwarta ke nan. Ya tabbatar da su ta wurin yin shiru sa’ad da ya ji ta.

  9. Ƙidaya 30:15kusan 1452 K.H.

    Amma in ya ji, sa’an nan daga baya ya hana ta, to, zai sha hukuncin laifinta.”

  10. Ƙidaya 30:16kusan 1452 K.H.

    Waɗannan su ne ƙa’idodin da Ubangiji ya ba wa Musa game da dangantakar miji da matarsa, da kuma tsakanin mahaifi da ’yarsa wadda har yanzu tana a gidansa.

  11. Ƙidaya 31:1kusan 1452 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  12. Ƙidaya 31:2kusan 1452 K.H.

    “Ka ɗaukar wa Isra’ilawa fansa, a kan Midiyawa. Bayan wannan za ka mutu, a kuwa tara ka ga mutanenka.”

  13. Ƙidaya 31:3kusan 1452 K.H.

    Saboda haka Musa ya ce wa mutane, “Ku shirya waɗansu daga cikin mazanku, su tafi su yi yaƙi da Midiyawa don su ɗaukar wa Ubangiji fansa a kansu.”

  14. Ƙidaya 31:4kusan 1452 K.H.

    Ku aiki maza dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila.

  15. Ƙidaya 31:5kusan 1452 K.H.

    Saboda haka aka samo mayaƙa dubu goma sha biyu shiryayyu don yaƙi, maza dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila.

  16. Ƙidaya 31:6kusan 1452 K.H.

    Musa ya aike su zuwa yaƙi, dubu ɗaya daga kowace kabila, tare da Finehas ɗan Eleyazar, firist, wanda ya ɗauki kayayyaki daga wuri mai tsarki da ƙahoni don kiran yaƙi.

  17. Ƙidaya 31:7kusan 1452 K.H.

    Suka yi yaƙi da Midiyawa, suka kashe kowane mutum yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  18. Ƙidaya 31:8kusan 1452 K.H.

    A cikin waɗanda aka kashe kuwa akwai Ewi, Rekem, Zur, Hur da Reba; sarakuna biyar na Mediyawa. Suka kuma kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi.

  19. Ƙidaya 31:9kusan 1452 K.H.

    Isra’ilawa suka kwashe mata da yaran Midiyawa, a matsayin bayi. Suka kwashe shanunsu da tumakinsu da kuma dukan dukiyarsu, a matsayin ganima.

  20. Ƙidaya 31:10kusan 1452 K.H.

    Suka ƙone dukan garuruwan da Midiyawa suke zama, da dukan sansaninsu.

  21. Ƙidaya 31:11kusan 1452 K.H.

    Suka kwashe dukan ganima haɗe da mutane da dabbobi,

  22. Ƙidaya 31:12kusan 1452 K.H.

    suka kawo bayi da ganiman nan, wurin Musa da Eleyazar firist, da kuma jama’ar Isra’ilawa, a sansaninsu a filayen Mowab kusa da Urdun daga ƙetaren Yeriko.

  23. Ƙidaya 31:13kusan 1452 K.H.

    Musa, da Eleyazar firist da dukan shugabannin jama’a, suka fito suka tarye su a bayan sansani.

  24. Ƙidaya 31:14kusan 1452 K.H.

    Musa kuwa ya husata da shugabannin sojojin da suke shugabannin dubbai da shugabannin ɗari-ɗarin da suka dawo daga yaƙi.

  25. Ƙidaya 31:15kusan 1452 K.H.

    Ya tambaye su ya ce, “Kun bar dukan mata da rai?