- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ƙidaya 31:41kusan 1452 K.H.
Musa ya ba wa Eleyazar abin da aka ware wa Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
- Ƙidaya 31:42kusan 1452 K.H.
Kashin da aka ba wa Isra’ilawa, wanda Musa ya ware daga cikin na waɗanda suka tafi yaƙi,
- Ƙidaya 31:43kusan 1452 K.H.
kashin da aka ba wa jama’a kuwa tumaki 337,500 ne,
- Ƙidaya 31:44kusan 1452 K.H.
shanu 36,000,
- Ƙidaya 31:45kusan 1452 K.H.
jakuna 30,500
- Ƙidaya 31:46kusan 1452 K.H.
da mutane 16,000.
- Ƙidaya 31:47kusan 1452 K.H.
Daga rabin kashi na Isra’ilawa, Musa ya ɗauki ɗaya daga cikin hamsin na mutane da na dabbobi, yadda Ubangiji ya umarce shi, ya ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji.
- Ƙidaya 31:48kusan 1452 K.H.
Sai shugabannin da suka shugabancin rundunar yaƙin, shugabanni na dubu-dubu da shugabanni na ɗari-ɗari, suka zo wurin Musa
- Ƙidaya 31:49kusan 1452 K.H.
suka ce masa, “Barorinka sun ƙidaya mayaƙan da suke ƙarƙashinmu, babu ko ɗayan ya ɓace.
- Ƙidaya 31:50kusan 1452 K.H.
Saboda haka mun kawo wa Ubangiji hadaya na kayan zinariya da kowannenmu ya samu, mundaye, ƙawane, ’yan kunne da duwatsun wuya, don yin wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.”
- Ƙidaya 31:51kusan 1452 K.H.
Musa da Eleyazar firist, suka karɓi zinariya da kayan adon duka daga gare su.
- Ƙidaya 31:52kusan 1452 K.H.
Dukan zinariya da shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, waɗanda Musa da Eleyazar suka karɓa, suka kuma miƙa hadaya ga Ubangiji, nauyinta ta kai shekel 16,750.
- Ƙidaya 31:53kusan 1452 K.H.
Kowane soja, ya kwashi ganima wa kansa.
- Ƙidaya 31:54kusan 1452 K.H.
Musa da Eleyazar firist, suka karɓi zinariya daga shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, suka kawo cikin Tentin Sujada, don su zama abin tuni ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji.
- Ƙidaya 32:1kusan 1452 K.H.
Mutanen Ruben da mutanen Gad, da suke da garken shanu da kuma garke tumaki masu yawa, suka ga cewa ƙasashen Yazer da Gileyad wurare ne masu kyau don kiwon shanu da tumaki.
- Ƙidaya 32:2kusan 1452 K.H.
Saboda haka suka zo wurin Musa da Eleyazar da kuma shugabannin jama’a, suka ce,
- Ƙidaya 32:3kusan 1452 K.H.
“Atarot, Dibon, Yazer, Nimra, Heshbon, Eleyale, Sebam, Nebo da Beyon,
- Ƙidaya 32:4kusan 1452 K.H.
ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban mutane Isra’ila, suna da kyau don dabbobi, bayinku kuma suna da dabbobi.”
- Ƙidaya 32:5kusan 1452 K.H.
Suka ce, “In mun sami tagomashi daga gare ka bari a ba da wannan ƙasa ga bayinka, tă zama mallakanmu. Kada ka sa mu haye Urdun.”
- Ƙidaya 32:6kusan 1452 K.H.
Musa ya ce wa mutanen Gad da mutanen Ruben, “Wato, sai ’yan’uwanku su yi ta yaƙi ku kuwa ku zauna nan?
- Ƙidaya 32:7kusan 1452 K.H.
Don me za ku karya zuciya Isra’ilawa daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su?
- Ƙidaya 32:8kusan 1452 K.H.
Haka iyayenku suka yi sa’ad da na aike su daga Kadesh Barneya don su dubo ƙasar.
- Ƙidaya 32:9kusan 1452 K.H.
Gama bayan suka haura Kwarin Eshkol suka hangi ƙasar, sai suka karya zuciyar Isra’ilawa daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su.
- Ƙidaya 32:10kusan 1452 K.H.
A ranar kuwa Ubangiji ya husata har ya yi wannan rantsuwa cewa,
- Ƙidaya 32:11kusan 1452 K.H.
‘Tabbatacce ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba, da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, domin ba su bi ni sosai ba,