Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 32:37kusan 1452 K.H.

    Mutanen Ruben suka sāke gina Heshbon, Eleyale, da Kiriyatayim,

  2. Ƙidaya 32:38kusan 1452 K.H.

    haka kuma suka gina Nebo da Ba’al-Meyon (an canja waɗannan sunaye) suka kuma gina Sibma. Suka ba wa biranen da suka sāke ginawa sunaye.

  3. Ƙidaya 32:39kusan 1452 K.H.

    Zuriyar Makir ɗan Manasse suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori mutanen Amoriyawa da suke can.

  4. Ƙidaya 32:40kusan 1452 K.H.

    Saboda haka Musa ya ba da Gileyad ga mutanen Makir, zuriyar Manasse, suka kuma zauna a can.

  5. Ƙidaya 32:41kusan 1452 K.H.

    Yayir, wani ɗan Manasse, ya ci ƙauyukansu da yaƙi, ya kuma ba su sunan Hawwot Yayir.

  6. Ƙidaya 32:42kusan 1452 K.H.

    Noba kuma ya ci Kenat da ƙauyukanta da yaƙi, ya kuma ba ta suna Noba, bisa ga sunansa.

  7. Ga wuraren da Isra’ilawa suka yi sansani sa’ad da suka fito runduna-runduna a ƙarƙashin Musa da Haruna daga Masar.

  8. Bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tafiye-tafiyensu da sansaninsu. Ga yadda tafiye-tafiyen suka kasance.

  9. Isra’ilawa sun tashi daga Rameses a rana ta goma sha biyar, ga watan fari, kashegarin Bikin Ƙetarewa. Suka fita gabagadi a gaban dukan Masarawa,

  10. waɗanda suke binne gawawwakin ’ya’yan farinsu da Ubangiji ya karkashe; gama Ubangiji ya hukunta allolinsu.

  11. Isra’ilawa suka tashi daga Rameses, suka yi sansani a Sukkot.

  12. Suka tashi daga Sukkot, suka yi sansani a Etam, a gefen hamada.

  13. Suka tashi daga Etam, suka koma baya zuwa Fi Hahirot, wajen gabashin Ba’al-Zafon, suka yi sansani kusa da Migdol.

  14. Suka tashi daga Fi Hahirot, suka ratsa cikin teku zuwa hamada, bayan sun yi tafiya kwana uku a cikin Hamadan Etam, sai suka yi sansani a Mara.

  15. Suka tashi daga Mara, suka tafi Elim, inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu, da itatuwan dabino guda saba’in, suka yi sansani a can.

  16. Suka tashi daga Elim, suka yi sansani kusa da Jan Teku.

  17. Suka tashi daga Jan Teku, suka yi sansani a Hamadan Sin.

  18. Suka tashi daga Hamadan Sin, suka yi sansani a Dofka.

  19. Suka tashi daga Dofka, suka yi sansani a Alush.

  20. Suka tashi daga Alush, suka yi sansani a Refidim, inda babu ruwan da mutane za su sha.

  21. Suka tashi daga Refidim, suka yi sansani a Hamadan Sinai.

  22. Suka tashi daga Hamadan Sinai, suka yi sansani a Kibrot Hatta’awa.

  23. Suka tashi daga Kibrot Hatta’awa, suka yi sansani a Hazerot.

  24. Suka tashi daga Hazerot, suka yi sansani a Ritma.

  25. Suka tashi daga Ritma, suka yi sansani a Rimmon Ferez.