Tsallake zuwa abun ciki

circa 1010–970 BC

The Reign of David

David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.

1,230 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Tarihi 11:17kusan 1055 K.H.

    Dawuda ya ji marmarin ruwan sha sai ya ce, “Kash, a ce wani zai sami mini ruwan sha daga rijiya kusa da ƙofar Betlehem mana!”

  2. 1 Tarihi 11:18kusan 1055 K.H.

    Sai Ukun suka kutsa kai cikin sansanin Filistiyawa, suka ja ruwa daga rijiyar da take kusa da ƙofar Betlehem suka ɗauko shi suka kawo wa Dawuda. Amma ya ƙi yă sha; a maimako, sai ya zubar da shi a gaban Ubangiji.

  3. 1 Tarihi 11:19kusan 1055 K.H.

    Ya ce, “Allah yă sawwaƙe in yi haka, ya kamata in sha jinin waɗannan mutanen da suka yi kasai da rayukansu?” Domin sun yi kasai da rayukansu don su dawo da shi, Dawuda bai sha shi ba. Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan.

  4. 1 Tarihi 11:20kusan 1055 K.H.

    Abishai ɗan’uwan Yowab shi ma babba ne cikin Ukun nan. Ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe, ya kuma zama sananne kamar Ukun.

  5. 1 Tarihi 11:21kusan 1055 K.H.

    Aka ninka girmama shi bisa Ukun, sai ya zama shugaba, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.

  6. 1 Tarihi 11:22kusan 1055 K.H.

    Benahiya ɗan Yehohiyada shi ma wani barden yaƙi ne daga Kabzeyel, wanda ya yi manyan abubuwa. Ya bugi gwanayen Mowab biyu. Ya kuma gangara zuwa cikin rami a ranar da aka yi dusar ƙanƙara ya kashe zaki.

  7. 1 Tarihi 11:23kusan 1055 K.H.

    Ya kuma kashe wani mutumin Masar mai tsayi ƙafa bakwai da rabi. Ko da yake mutumin Masar yana da māshi kamar sandan masaƙa a hannunsa, Benahiya ya yaƙe shi da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannun mutumin Masar ya kuma kashe shi da māshin nan nasa.

  8. 1 Tarihi 11:24kusan 1055 K.H.

    Irin abubuwan da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma sananne ne kamar waɗannan jarumawa uku.

  9. 1 Tarihi 11:25kusan 1055 K.H.

    Aka ɗauka shi da bangirma fiye da Talatin nan, amma ba a haɗa shi cikin Ukun ba. Dawuda kuwa ya sa shi yă lura da masu tsaron lafiyarsa.

  10. 1 Tarihi 11:26kusan 1055 K.H.

    Jarumawan nan su ne, Asahel ɗan’uwan Yowab, Elhanan ɗan Dodo daga Betlehem,

  11. 1 Tarihi 11:27kusan 1055 K.H.

    Shammot mutumin Haror, Helez mutumin Felon,

  12. 1 Tarihi 11:28kusan 1055 K.H.

    Ira ɗan Ikkesh daga Tekowa, Abiyezer daga Anatot,

  13. 1 Tarihi 11:29kusan 1055 K.H.

    Sibbekai mutumin Husha, Ilai mutumin Aho,

  14. 1 Tarihi 11:30kusan 1055 K.H.

    Maharai mutumin Netofa, Heled ɗan Ba’ana mutumin Netofa,

  15. 1 Tarihi 11:31kusan 1055 K.H.

    Ittai ɗan Ribai daga Gibeya a Benyamin, Benahiya mutumin Firaton,

  16. 1 Tarihi 11:32kusan 1055 K.H.

    Hurai daga kogunan Ga’ash, Abiyel mutumin Arba,

  17. 1 Tarihi 11:33kusan 1055 K.H.

    Azmawet mutumin Harum, Eliyaba mutumin Sha’albo,

  18. 1 Tarihi 11:34kusan 1055 K.H.

    ’ya’yan Hashem mutumin Gizon maza, Yonatan ɗan Shageye mutumin Harar,

  19. 1 Tarihi 11:35kusan 1055 K.H.

    Ahiyam ɗan Sakar mutumin Harar, Elifal ɗan Ur,

  20. 1 Tarihi 11:36kusan 1055 K.H.

    Hefer mutumin Mekerat, Ahiya mutumin Felon,

  21. 1 Tarihi 11:37kusan 1055 K.H.

    Hezro mutumin Karmel, Na’arai ɗan Ezbai,

  22. 1 Tarihi 11:38kusan 1055 K.H.

    Yowel ɗan’uwan Natan, Mibhar ɗan Hagiri,

  23. 1 Tarihi 11:39kusan 1055 K.H.

    Zelek mutumin Ammon Naharai Baroti, mai ɗaukar kayan yaƙin Yowab ɗan Zeruhiya,

  24. 1 Tarihi 11:40kusan 1055 K.H.

    Ira mutumin Itra, Gareb mutumin Itra,

  25. 1 Tarihi 11:41kusan 1055 K.H.

    Uriya mutumin Hitti Zabad ɗan Alai,