Tsallake zuwa abun ciki

circa 1010–970 BC

The Reign of David

David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.

1,230 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Da Dawuda ya tafi Ziklag, waɗannan mutanen Manasse ne suka haɗa kai da shi. Adna, Yozabad, Yediyayel, Mika’ilu, Yozabad, Elihu da Zilletai, shugabannin ƙungiyoyi na dubu a cikin Manasse.

  2. Suka taimaki Dawuda a kan ƙungiyoyin hari, gama dukansu jarumawa ne sosai, kuma su shugabanni ne a cikin mayaƙansa.

  3. Kowace rana mutane suka riƙa zuwa don su taimaki Dawuda, sai da ya kasance da runduna mai girma, kamar mayaƙan Allah.

  4. 1 Tarihi 12:23kusan 1048 K.H.

    Ga yawan mutanen shiryayyu don yaƙi waɗanda suka zo wurin Dawuda a Hebron don su mai da mulkin Shawulu gare shi, yadda Ubangiji ya faɗa.

  5. 1 Tarihi 12:24kusan 1048 K.H.

    Mutanen Yahuda, masu riƙe garkuwa da māshi, su 6,800 shiryayyu don yaƙi;

  6. 1 Tarihi 12:25kusan 1048 K.H.

    mutanen Simeyon, jarumawa shiryayyu don yaƙi, su 7,100;

  7. 1 Tarihi 12:26kusan 1048 K.H.

    mutanen Lawi, su 4,600,

  8. 1 Tarihi 12:27kusan 1048 K.H.

    haɗe da Yehohiyada, shugaban iyalin Haruna tare da mutane 3,700,

  9. 1 Tarihi 12:28kusan 1048 K.H.

    da Zadok, matashi jarumi sosai, tare da shugabanni su 22 daga iyalinsa;

  10. 1 Tarihi 12:29kusan 1048 K.H.

    mutanen Benyamin, ’yan’uwan Shawulu, su 3,000, yawanci waɗanda suke biyayya ga gidan Shawulu sai lokacin;

  11. 1 Tarihi 12:30kusan 1048 K.H.

    mutanen Efraim, jarumawa, sanannu cikin gidajensu, su 20 800;

  12. 1 Tarihi 12:31kusan 1048 K.H.

    mutanen rabin kabilar Manasse, sanannu da sunaye suka zo suka mai da Dawuda sarki, su 18,000;

  13. 1 Tarihi 12:32kusan 1048 K.H.

    mutanen Issakar, masu fahimtar lokuta suka kuma san abin da ya kamata Isra’ila ya yi, manya 200, tare da danginsu a ƙarƙashin shugabancinsu;

  14. 1 Tarihi 12:33kusan 1048 K.H.

    mutanen Zebulun, ƙwararru sojoji shiryayyu don yaƙi da kowane irin makami, suka zo don su taimaki Dawuda da zuciya ɗaya, su 50,000;

  15. 1 Tarihi 12:34kusan 1048 K.H.

    mutanen Naftali su 1,000 shugabanni, tare da mutane 37,000 masu riƙe garkuwa da masu;

  16. 1 Tarihi 12:35kusan 1048 K.H.

    mutanen Dan, shiryayyu don yaƙi, su 28,600;

  17. 1 Tarihi 12:36kusan 1048 K.H.

    mutanen Asher, ƙwararrun sojoji shiryayyu don yaƙi, su 40,000;

  18. 1 Tarihi 12:37kusan 1048 K.H.

    kuma daga gabashin Urdun, mutanen Ruben, Gad da kuma rabin kabilar Manasse, masu kayan yaƙi iri-iri, su 120,000.

  19. 1 Tarihi 12:38kusan 1048 K.H.

    Dukan waɗannan mayaƙa ne waɗanda suka ba da kansu da yardar rai su yi hidima. Suka zo Hebron da cikakken niyya don su naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila. Duka sauran Isra’ilawa su ma suka goyi baya a naɗa Dawuda sarki.

  20. 1 Tarihi 12:39kusan 1048 K.H.

    Mutanen suka yi kwana uku a can tare da Dawuda, suna ci suna sha, gama iyalansu sun yi musu tanadi.

  21. 1 Tarihi 12:40kusan 1048 K.H.

    Haka ma, maƙwabtansu daga nesa har Issakar, Zebulun da Naftali suka zo suka kawo abinci a kan jakuna, raƙuma, alfadarai da shanu. Akwai tanadin mai yawa na gari, kauɗar ɓaure, nonnan busassun ’ya’yan inabi, ruwan inabi, mai, shanu da tumaki. Duk an yi haka don a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra’ila.

  22. Sai Dawuda ya tattauna da kowane ɗaya daga cikin shugabanninsa, shugabannin sojoji na dubu-dubu da na ɗari-ɗari.

  23. Sa’an nan ya ce wa dukan taron Isra’ila, “In ya yi muku kyau kuma in nufin Ubangiji Allahnmu ne, bari mu aika da saƙo nesa da kuma ko’ina zuwa ga sauran ’yan’uwanmu a duk iyakokin Isra’ila, da kuma zuwa ga firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a garuruwansu da makiyayansu, su zo wurinmu.

  24. Bari mu ɗauko akwatin alkawarin Allahnmu mu kawo wurinmu, gama ba mu neme shi a lokacin mulkin Shawulu ba.”

  25. Dukan taron jama’a suka yarda su yi haka, domin ya yi daidai ga dukan mutane.