Tsallake zuwa abun ciki

circa 1010–970 BC

The Reign of David

David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.

1,230 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Tarihi 14:16kusan 1047 K.H.

    Saboda haka Dawuda ya yi kamar yadda Allah ya umarce shi, suka kuma bugi mayaƙan Filistiyawa, tun daga Gibeyon har zuwa Gezer.

  2. 1 Tarihi 14:17kusan 1047 K.H.

    Sai sunan Dawuda ya bazu ko’ina a ƙasar, Ubangiji kuwa ya sa dukan al’ummai suka ji tsoronsa.

  3. 1 Tarihi 15:1kusan 1042 K.H.

    Bayan Dawuda ya yi gine-gine wa kansa a Birnin Dawuda, sai ya shirya wuri domin akwatin alkawarin Allah, ya kuma kafa tenti dominsa.

  4. 1 Tarihi 15:2kusan 1042 K.H.

    Sa’an nan Dawuda ya ce, “Babu wani sai ko Lawiyawa kaɗai za su ɗauka akwatin alkawarin Allah, gama Ubangiji ya zaɓe su su ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji su kuma yi hidima a gabansa har abada.”

  5. 1 Tarihi 15:3kusan 1042 K.H.

    Dawuda ya tattara dukan Isra’ila a Urushalima don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurin da aka shirya dominsa.

  6. 1 Tarihi 15:4kusan 1042 K.H.

    Ya tattara zuriyar Haruna a wuri ɗaya da kuma Lawiyawa.

  7. 1 Tarihi 15:5kusan 1042 K.H.

    Daga zuriyar Kohat, Uriyel shugaba da dangi 120;

  8. 1 Tarihi 15:6kusan 1042 K.H.

    daga zuriyar Merari Asahiya shugaba da dangi 220;

  9. 1 Tarihi 15:7kusan 1042 K.H.

    daga zuriyar Gershom, Yowel shugaba da dangi 130;

  10. 1 Tarihi 15:8kusan 1042 K.H.

    daga zuriyar Elizafan, Shemahiya shugaba da dangi 200;

  11. 1 Tarihi 15:9kusan 1042 K.H.

    daga zuriyar Hebron, Eliyel shugaba da dangi 80;

  12. 1 Tarihi 15:10kusan 1042 K.H.

    daga zuriyar Uzziyel, Amminadab shugaba da dangi 112.

  13. 1 Tarihi 15:11kusan 1042 K.H.

    Sa’an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyatar, firistoci, tare da Uriyel, Asahiya, Yowel, Shemahiya, Eliyel da Amminadab, Lawiyawa.

  14. 1 Tarihi 15:12kusan 1042 K.H.

    Ya ce musu, “Ku ne kawunan iyalan Lawiyawa; ku da ’yan’uwanku Lawiyawa, sai ku tsarkake kanku ku hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila, zuwa wurin da na shirya dominsa.

  15. 1 Tarihi 15:13kusan 1042 K.H.

    Domin ku, Lawiyawa ba ku haura da shi da farko ba ne ya sa Ubangiji Allahnmu ya husata a kanmu. Ba mu tambaye shi game da yadda za mu yi shi a hanyar da aka ƙayyade ba.”

  16. 1 Tarihi 15:14kusan 1042 K.H.

    Saboda haka firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu don su hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  17. 1 Tarihi 15:15kusan 1042 K.H.

    Sai Lawiyawa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah da sanduna a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji.

  18. 1 Tarihi 15:16kusan 1042 K.H.

    Dawuda ya faɗa wa shugabannin Lawiyawa su sa ’yan’uwansu su zama mawaƙa don su rera waƙoƙi masu farin ciki, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, molaye, garayu da ganguna.

  19. 1 Tarihi 15:17kusan 1042 K.H.

    Saboda haka Lawiyawa suka zaɓi Heman ɗan Yowel, da Asaf ɗan Berekiya daga cikin ’yan’uwansu. Daga iyalin Merari kuma aka zaɓi Etan ɗan Kushahiya.

  20. 1 Tarihi 15:18kusan 1042 K.H.

    Tare da su kuma ’yan’uwansa da suke biye bisa ga matsayi. Wato, Zakariya, Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ben, Ma’asehiya, Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom da Yehiyel, matsaran ƙofofi.

  21. 1 Tarihi 15:19kusan 1042 K.H.

    Mawaƙan nan Heman, Asaf da Etan, ne za su buga kugen tagulla.

  22. 1 Tarihi 15:20kusan 1042 K.H.

    Zakariya, Aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ma’asehiya da Benahiya, ne za su kaɗa molaye masu murya sama-sama, bisa ga alamot.

  23. 1 Tarihi 15:21kusan 1042 K.H.

    Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom, Yehiyel da Azaziya, ne za su ja garayu masu murya ƙasa-ƙasa bisa ga sheminit.

  24. 1 Tarihi 15:22kusan 1042 K.H.

    Kenaniya, shugaban Lawiyawa, shi ne mai bi da waƙoƙi. Wannan hakkinsa ne, gama shi gwani ne a wannan fanni.

  25. 1 Tarihi 15:23kusan 1042 K.H.

    Berekiya da Elkana, ne za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin.