- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Tarihi 15:24kusan 1042 K.H.
Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zakariya, Benahiya da Eliyezer firistoci, su ne za su busa ƙahoni a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-Edom da Yehiya su ma za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin.
- 1 Tarihi 15:25kusan 1042 K.H.
Sai Dawuda da dattawan Isra’ila da shugabannin ƙungiyoyi dubu suka haura don su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-Edom, da farin ciki.
- 1 Tarihi 15:26kusan 1042 K.H.
Domin Allah ya taimaki Lawiyawan da suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, aka miƙa hadayar bijimai bakwai da raguna bakwai.
- 1 Tarihi 15:27kusan 1042 K.H.
To, fa, Dawuda yana saye da kyakkyawar rigar lilin, kamar yadda dukan Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin suka sa, da kuma yadda mawaƙa, da Kenaniya, wanda yake bi da waƙar mawaƙan ya sa. Dawuda kuma ya sa efod lilin.
- 1 Tarihi 15:28kusan 1042 K.H.
Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu.
- 1 Tarihi 15:29kusan 1042 K.H.
Yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yake shiga Birnin Dawuda, Mikal ’yar Shawulu ta leƙa daga taga. Sa’ad da ta ga Sarki Dawuda yana rawa yana shagali, sai ta rena masa wayo a zuciyarta.
- 1 Tarihi 16:1kusan 1042 K.H.
Suka fa kawo akwatin alkawarin Allah, suka sa a cikin tentin da Dawuda ya kafa dominsa, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa da hadayu na salama a gaban Allah.
- 1 Tarihi 16:2kusan 1042 K.H.
Bayan Dawuda ya gama miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji.
- 1 Tarihi 16:3kusan 1042 K.H.
Sa’an nan ya ba da dunƙulen burodi da wainar dabino da kuma kauɗar zabibi ga kowane mutumin Isra’ila namiji da ta mace.
- 1 Tarihi 16:4kusan 1042 K.H.
Ya sa Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka, su gode, su kuma yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila.
- 1 Tarihi 16:5kusan 1042 K.H.
Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna,
- 1 Tarihi 16:6kusan 1042 K.H.
Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah.
- 1 Tarihi 16:7kusan 1042 K.H.
A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da ’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji.
- 1 Tarihi 16:8kusan 1042 K.H.
Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
- 1 Tarihi 16:9kusan 1042 K.H.
Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa.
- 1 Tarihi 16:10kusan 1042 K.H.
Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
- 1 Tarihi 16:11kusan 1042 K.H.
Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum.
- 1 Tarihi 16:12kusan 1042 K.H.
Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata, mu’ujizansa da kuma hukuntai da ya yanke,
- 1 Tarihi 16:13kusan 1042 K.H.
Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub maza, zaɓaɓɓunsa.
- 1 Tarihi 16:14kusan 1042 K.H.
Shi ne Ubangiji Allahnmu; hukuntansa suna a cikin dukan duniya.
- 1 Tarihi 16:15kusan 1042 K.H.
Yakan tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,
- 1 Tarihi 16:16kusan 1042 K.H.
alkawarin da ya yi wa Ibrahim rantsuwar da ya yi ga Ishaku.
- 1 Tarihi 16:17kusan 1042 K.H.
Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida, ga Isra’ila kamar madawwamin alkawari.
- 1 Tarihi 16:18kusan 1042 K.H.
“Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana kamar rabon da za ka gāda.”
- 1 Tarihi 16:19kusan 1042 K.H.
Sa’ad da suke kima, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,