Tsallake zuwa abun ciki

circa 1010–970 BC

The Reign of David

David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.

1,230 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Tarihi 17:2kusan 1042 K.H.

    Natan ya amsa wa Dawuda ya ce, “Duk abin da kake tunani a zuciya, ka yi, gama Allah yana tare da kai.”

  2. 1 Tarihi 17:3kusan 1042 K.H.

    A daren nan maganar Allah ta zo wa Natan cewa,

  3. 1 Tarihi 17:4kusan 1042 K.H.

    “Ka tafi ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ba kai ba ne za ka gida mini gidan da zan zauna a ciki.

  4. 1 Tarihi 17:5kusan 1042 K.H.

    Ban taɓa zama a gida daga ranar da na fito da Isra’ila daga Masar ba har wa yau. Na yi ta yawo daga gefen da aka kafa tenti zuwa wani, daga wannan wuri zuwa wancan.

  5. 1 Tarihi 17:6kusan 1042 K.H.

    Duk inda na tafi tare da Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani daga cikin shugabanninsu waɗanda na umarta su yi kiwon mutanena, “Don me ba ku gida mini gidan al’ul ba?” ’

  6. 1 Tarihi 17:7kusan 1042 K.H.

    “Yanzu, ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauke ka daga makiyaya da kuma daga bin garke, don ka zama mai mulki a bisa mutanena Isra’ila.

  7. 1 Tarihi 17:8kusan 1042 K.H.

    Na kasance tare da kai ko’ina ka tafi, na kuma yanke dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka kamar sunayen mutane mafi girma na duniya.

  8. 1 Tarihi 17:9kusan 1042 K.H.

    Zan kuma tanada wuri domin mutanena Isra’ila, zan kuma kafa su saboda za su kasance da gidan kansu ba kuwa za a ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara zaluntar su ba, yadda suka yi da farko

  9. 1 Tarihi 17:10kusan 1042 K.H.

    da kuma suka yi tun lokacin da na sa shugabanni a bisa mutanen Isra’ila. Zan rinjaye dukan abokan gābanka. “ ‘Na furta maka cewa Ubangiji zai gina maka gida,

  10. 1 Tarihi 17:11kusan 1042 K.H.

    sa’ad da kwanakinka suka ƙare ka kuma tafi don ka kasance da kakanninka, zan tā da ɗaya cikin ’ya’yanka maza, daga zuriyarka yă gāje ka, zan kuma kafa mulkinka.

  11. 1 Tarihi 17:12kusan 1042 K.H.

    Shi ne zai gina gida domina, zan kuma kafa sarautarsa har abada.

  12. 1 Tarihi 17:13kusan 1042 K.H.

    Zan zama Ubansa, zai kuma zama ɗana. Ba zan taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi, kamar yadda na ɗauke ta daga wanda ya riga ka ba.

  13. 1 Tarihi 17:14kusan 1042 K.H.

    Zan sa shi a bisa gidana da mulkina har abada; kujerar sarautarsa za tă kahu har abada.’ ”

  14. 1 Tarihi 17:15kusan 1042 K.H.

    Natan ya faɗa wa Dawuda dukan kalmomin wahayin nan.

  15. 1 Tarihi 17:16kusan 1042 K.H.

    Sai Sarki Dawuda ya shiga ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Allah, kuma wane ne iyalina, da ka kawo ni har zuwa nan?

  16. 1 Tarihi 17:17kusan 1042 K.H.

    Kuma sai ka ce wannan bai isa ba a idonka, ya Allah, ka yi magana game da nan gaba na gidan bawanka. Ka dube ni sai ka ce ni ne mafi ɗaukaka cikin mutane, ya Ubangiji Allah.

  17. 1 Tarihi 17:18kusan 1042 K.H.

    “Me kuma Dawuda zai ce maka saboda girmamawar da ka yi wa bawanka? Gama ka san bawanka,

  18. 1 Tarihi 17:19kusan 1042 K.H.

    Ya Ubangiji. Gama saboda bawanka da kuma bisa ga nufinka, ka yi wannan babban abu, ka kuma sanar da dukan manyan alkawura.

  19. 1 Tarihi 17:20kusan 1042 K.H.

    “Babu wani kamar ka, ya Ubangiji, babu kuma Allah sai kai, kamar yadda muka ji da kunnuwanmu.

  20. 1 Tarihi 17:21kusan 1042 K.H.

    Wane ne kuma yake kamar mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allahnta ya fita don yă fanshi mutane wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa masu banmamaki masu banrazana ta wurin korin al’ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka fansa daga Masar?

  21. 1 Tarihi 17:22kusan 1042 K.H.

    Ka mai da mutanenka Isra’ila na kanka har abada, kuma kai, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.

  22. 1 Tarihi 17:23kusan 1042 K.H.

    “Yanzu kuwa, Ubangiji, bari alkawarin da ka yi game da bawanka da gidansa yă kahu har abada. Yi kamar yadda ka yi alkawari,

  23. 1 Tarihi 17:24kusan 1042 K.H.

    saboda zai kahu kuma sunanka zai zama mai girma har abada. Sa’an nan mutane za su ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki, Allah a bisa Isra’ila, Allahn Isra’ila ne!’ Kuma gidan bawanka Dawuda zai kahu a gabanka.

  24. 1 Tarihi 17:25kusan 1042 K.H.

    “Kai, Allahna, ka bayyana ga bawanka cewa za ka gina gida dominsa. Ta haka bawanka ya sami ƙarfin gwiwa ya yi addu’a gare ka.

  25. 1 Tarihi 17:26kusan 1042 K.H.

    Ya Ubangiji, kai ne Allah! Ka yi alkawari abubuwa masu kyau wa bawanka.