Tsallake zuwa abun ciki

circa 1010–970 BC

The Reign of David

David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.

1,230 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Tarihi 17:27kusan 1042 K.H.

    Yanzu ka ji daɗi don ka albarkace gidan bawanka, don yă ci gaba har abada a gabanka; gama kai, ya Ubangiji, ka albarkace shi, ya kuma sami albarka ke nan har abada.”

  2. 1 Tarihi 18:1kusan 1040 K.H.

    Ana nan sai Dawuda ya ci Filistiyawa ya kuma rinjaye su, ya ƙwace Gat da ƙauyukan kewayenta daga mulkin Filistiyawa.

  3. 1 Tarihi 18:2kusan 1040 K.H.

    Dawuda ya kuma ci Mowabawa, suka zama bayinsa suka kuma biya haraji.

  4. 1 Tarihi 18:3kusan 1040 K.H.

    Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer sarkin Zoba, har can Hamat, sa’ad da ya je don yă kafa mulkinsa a wajen Kogin Yuferites.

  5. 1 Tarihi 18:4kusan 1040 K.H.

    Dawuda ya kame keken yaƙinsa dubu ɗaya, da mahayan kekunan yaƙi dubu bakwai da sojojin kafa guda dubu ashirin. Ya yayyanke dukan agaran dawakansa, amma ya bar dawakai da suka isa jan kekunan yaƙi ɗari.

  6. 1 Tarihi 18:5kusan 1040 K.H.

    Da Arameyawan Damaskus suka zo su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya bugi dubu ashirin da biyunsu.

  7. 1 Tarihi 18:6kusan 1040 K.H.

    Ya sa ƙungiyoyin sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus. Arameyawan kuwa suka zama bayinsa, suka kuma kawo haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi.

  8. 1 Tarihi 18:7kusan 1040 K.H.

    Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariyan da shugabannin sojojin Hadadezer suke riƙe, ya kawo su Urushalima.

  9. 1 Tarihi 18:8kusan 1040 K.H.

    Daga Teba da Kun, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Dawuda ya kwashe tagulla da yawa sosai, wanda Solomon ya yi amfani don yă yi Tekun tagulla, ginshiƙai da kuma kayayyakin tagulla dabam-dabam.

  10. 1 Tarihi 18:9kusan 1040 K.H.

    Sa’ad da Towu sarkin Hamat ya ji cewa Dawuda ya ci mayaƙan Hadadezer sarkin Zoba gaba ɗaya,

  11. 1 Tarihi 18:10kusan 1040 K.H.

    sai ya aiki ɗansa Hadoram zuwa wurin Sarki Dawuda yă gaishe shi yă kuma yi masa barka da nasara a yaƙi a kan Hadadezer, wanda yake yaƙi da Towu. Hadoram ya kawo kowane irin kayayyakin zinariya da na azurfa da na tagulla.

  12. 1 Tarihi 18:11kusan 1040 K.H.

    Sarki Dawuda ya miƙa waɗannan kayayyakin ga Ubangiji, kamar yadda ya yi da azurfa da kuma zinariyan da ya kwaso daga dukan waɗannan al’ummai. Edom da Mowab, Ammonawa da Filistiyawa, da kuma Amalek.

  13. 1 Tarihi 18:12kusan 1040 K.H.

    Abishai ɗan Zeruhiya ya bugi mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri.

  14. 1 Tarihi 18:13kusan 1040 K.H.

    Ya sa ƙungiyoyin sojoji a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi.

  15. 1 Tarihi 18:14kusan 1040 K.H.

    Dawuda ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila, yana yin abin da yake daidai da kuma gaskiya saboda dukan mutanensa.

  16. 1 Tarihi 18:15kusan 1040 K.H.

    Yowab ɗan Zeruhiya shi ne shugaban mayaƙa; Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci;

  17. 1 Tarihi 18:16kusan 1040 K.H.

    Zadok ɗan Ahitub da Abimelek ɗan Abiyatar su ne firistoci; Shafsha shi ne magatakarda;

  18. 1 Tarihi 18:17kusan 1040 K.H.

    Benahiya ɗan Yehohiyada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa; ’ya’yan Dawuda maza su ne manyan ma’aikata a gefen sarki.

  19. Ana nan, sai Nahash sarkin Ammonawa ya mutu, sai ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  20. Dawuda ya yi tunani, “Zan nuna jinƙai ga Hanun ɗan Nahash, domin mahaifinsa ya nuna alheri gare ni.” Saboda haka Dawuda ya aika da tawaga don yă yi wa Hanun ta’aziyya game da mahaifinsa. Sa’ad da mutanen Dawuda suka iso wurin Hanun a ƙasar Ammonawa don su ta’azantar da shi,

  21. sai manyan Ammonawa suka ce wa Hanun, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aika mutanen nan wurinka su ta’azantar da kai? Ba mutanensa sun zo ne su bincika su kuma leƙi ƙasar su tumɓuke ta ba?”

  22. Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda, ya yi musu aski, ya yayyanka rigunansu a daidai ɗuwawunsu, sa’an nan ya sallame su.

  23. Da wani ya zo ya faɗa wa Dawuda game da mutanen, sai ya aiki ’yan aika su sadu da su, gama an ƙasƙantar da su ainun. Sarki ya ce, “Ku zauna a Yeriko har sai gemunku sun yi girma, sa’an nan ku dawo.”

  24. Sa’ad da Ammonawa suka gane cewa sun zama abin wurin a kafan hancin Dawuda, Hanun da Ammonawa suka aika da talenti dubu na azurfa don su yi haya da kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi daga Aram-Naharayim, Aram Ma’aka da Zoba.

  25. Suka yi hayar kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi dubu talatin da biyu, da kuma sarkin Ma’aka tare da mayaƙansa, waɗanda suka zo suka kafa sansani kusa da Medeba, yayinda Ammonawa suka tattaru daga garuruwansu suka fita yaƙi.