- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Tarihi 16:20kusan 1042 K.H.
suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga wannan mulki zuwa wancan.
- 1 Tarihi 16:21kusan 1042 K.H.
Bai bar wani ya zalunce su ba; saboda su ya tsawata wa sarakuna.
- 1 Tarihi 16:22kusan 1042 K.H.
“Kada ku taɓa shafaffuna; kada ku yi wa annabawana lahani.”
- 1 Tarihi 16:23kusan 1042 K.H.
Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka; ku yi shelar cetonsa kowace rana.
- 1 Tarihi 16:24kusan 1042 K.H.
Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane.
- 1 Tarihi 16:25kusan 1042 K.H.
Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo; dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.
- 1 Tarihi 16:26kusan 1042 K.H.
Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ya yi sammai.
- 1 Tarihi 16:27kusan 1042 K.H.
Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da farin ciki suna a wurin zamansa.
- 1 Tarihi 16:28kusan 1042 K.H.
Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai, ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji,
- 1 Tarihi 16:29kusan 1042 K.H.
ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa. Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa; ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa.
- 1 Tarihi 16:30kusan 1042 K.H.
Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka! Duniya ta kahu sosai; ba za tă jijjigu ba.
- 1 Tarihi 16:31kusan 1042 K.H.
Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari su ce a cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki!”
- 1 Tarihi 16:32kusan 1042 K.H.
Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri; bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki!
- 1 Tarihi 16:33kusan 1042 K.H.
Sa’an nan itatuwan jeji za su rera, za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji, gama ya zo don yă hukunta duniya.
- 1 Tarihi 16:34kusan 1042 K.H.
Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne; ƙaunarsa madawwamiya ce.
- 1 Tarihi 16:35kusan 1042 K.H.
Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu; tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai, don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki, don mu ɗaukaka a cikin yabonka.”
- 1 Tarihi 16:36kusan 1042 K.H.
Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.”
- 1 Tarihi 16:37kusan 1042 K.H.
Dawuda ya bar Asaf da ’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana.
- 1 Tarihi 16:38kusan 1042 K.H.
Ya kuma bar Obed-Edom da ’yan’uwansa sittin da takwas don su yi hidima tare. Obed-Edom ɗan Yedutun da Hosa kuma, su ne matsaran ƙofofi.
- 1 Tarihi 16:39kusan 1042 K.H.
Dawuda ya bar Zadok firist da ’yan’uwansa firistoci a gaban tabanakul na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon
- 1 Tarihi 16:40kusan 1042 K.H.
don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila.
- 1 Tarihi 16:41kusan 1042 K.H.
Tare da su akwai Heman da Yedutun da sauran waɗannan zaɓaɓɓun da aka rubuta sunansu don yin godiya ga Ubangiji, “gama ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
- 1 Tarihi 16:42kusan 1042 K.H.
Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki. ’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa.
- 1 Tarihi 16:43kusan 1042 K.H.
Sa’an nan dukan mutanen suka tashi, kowa ya koma gidansa, Dawuda ya koma gida yă sa wa iyalinsa albarka.
- 1 Tarihi 17:1kusan 1042 K.H.
Bayan Dawuda ya zauna a fadansa, sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar da aka yi da al’ul, yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yana a ƙarƙashin tenti.”