Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Water

197 ayoyi · 84 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yayinda ɗayansu yake cikin saran itace, sai kan gatarin ya fāɗi a ruwa, sai ya ce, “Kash, ranka yă daɗe, kayan aro ne fa!”

  2. Sai mutumin Allah ya ce, “Daidai ina ya fāɗa?” Da ya nuna masa wurin, sai Elisha ya yanka ɗan sanda ya jefa a wurin, ya sa kan gatarin ya taso sama.

  3. Game da sauran ayyukan mulkin Hezekiya, dukan nasarorinsa da yadda ya yi tafki da kuma bututun ruwa inda ya kawo ruwa cikin birni, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

  4. sai ya yi shawara da fadawansa da hafsoshin mayaƙansa cewa su datse ruwa daga maɓulɓulan ruwan da yake waje da birnin, suka kuwa taimake shi.

  5. Sa’an nan na ci gaba zuwa wajen Ƙofar Maɓuɓɓuga da kuma Tafkin Sarki, amma babu isashen wuri saboda abin da na hau yă bi;

  6. Ko kyauro zai iya yi girma a wurin da ba ruwa? Ko za tă taɓa iya yin girma ba tare da ruwa ba?

  7. Daga ya ji ƙanshin ruwa zai tohu yă yi tsiro kamar shuka.

  8. yadda ruwa yakan zaizaye duwatsu ruwa mai ƙarfi kuma yă kwashe turɓayar ƙasa, haka kake barin mutum ba bege.

  9. Ba ka ba masu jin ƙishirwa su sha ba kuma ka hana wa masu jin yunwa abinci su ci.

  10. “Duk da haka kamar abu marar nauyi suke a kan ruwa; gefen ƙasar da suke, an la’anta ta, yadda ba wanda yake zuwa gonar inabinsu.

  11. Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa, duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba.

  12. Ya rufe fuskar wata, ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,

  13. Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara? Wane ne ya haifi jaura daga sammai

  14. An zubar da ni kamar ruwa, kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai. Zuciyata ta zama kaki; ta narke a cikina.

  15. Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa, yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,

  16. Bari su ɓace kamar ruwa mai wucewa; sa’ad da suka ja bakansu, bari kibiyoyinsu su murtsuke.

  17. Ka bar mutane suka hau a kawunanmu; mun bi ta wuta da ruwa, amma ka kawo mu zuwa wurin yalwa.

  18. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin.” Ta Dawuda. Ka cece ni, ya Allah, gama ruwa ya kai wuyata

  19. ya fid da rafuffuka daga dutsen da ya tsaga ya sa ruwa ya gudu kamar koguna.

  20. Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa; sun mamaye ni ɗungum.

  21. suka gudu a bisa duwatsu, suka gangara zuwa cikin kwaruruka, zuwa wurin da ka shirya musu.

  22. Ya sa la’antarwa kamar rigarsa; ta shiga cikin jikinsa kamar ruwa, cikin ƙasusuwansa kamar mai.

  23. da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu.

  24. Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf.

  25. Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu yă kuma watsar da hazo kamar toka.