Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Water: The sea
Ayoyi game da The sea
Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance.
Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.
Ba za su yi lahani ko su hallaka wani a dutsena mai tsarki ba, gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji kamar yadda ruwaye suka rufe teku.