Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Water: Symbolic

6 ayoyi · 84 fannoni

Ayoyi game da Symbolic

  1. saboda haka Ubangiji yana shirin yă kawo musu rigyawar ruwan Kogi, wato, sarkin Assuriya da dukan sojojinsa. Zai cika dukan gaɓoɓinsa, yă kuma malala har zuwa bakin kogi.

  2. sunan tauraron kuwa Maɗaci. Kashi ɗaya bisa uku na ruwaye ya zama mai ɗaci, mutane da yawa kuma suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.

  3. Sa’an nan daga bakinsa macijin ya kwarara ruwa kamar kogi, don ruwan ya cimma matan yă kuma kwashe ta tare da ambaliya.

  4. Mala’ika na uku ya juye kwanonsa a bisan koguna da maɓulɓulan ruwa, sai suka zama jini.

  5. Ɗaya daga cikin mala’iku bakwai masu ɗauke da kwanoni bakwai nan, ya zo ya ce mini, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwan nan da take zaune a bisan ruwaye masu yawa.

  6. Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Ruwayen da ka gani, inda karuwan take zama, jama’a ce, taro masu yawa, al’ummai da kuma harsuna.