Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Water: The want of, considered a great calamity

7 ayoyi · 84 fannoni

Ayoyi game da The want of, considered a great calamity

  1. Dukan taron Isra’ilawa suka kama tafiya daga Hamadar Sin, suka yi ta tafiya suna sauka a wurare dabam-dabam bisa ga umarnin Ubangiji. A ƙarshe suka sauka a Refidim, suka zauna a can, amma ba ruwan da jama’a za su sha.

  2. Saboda haka suka yi wa Musa maganganun banza suka ce, “Ba mu ruwa mu sha.” Musa ya amsa ya ce, “Don me kuke mini maganganun banza? Don me kuke gwada Ubangiji?”

  3. Amma mutanen suka yi fama da ƙishirwa a can, suka yi gunaguni a kan Musa. Suka ce, “Don me ka fitar da mu daga Masar, ka sa mu da ’ya’yanmu da dabbobinmu, mu mutu da ƙishirwa?”

  4. Sai aka rasa ruwa da jama’a za su sha, mutane suka taru, suka tayar wa Musa da Haruna.

  5. Saboda haka sarkin Isra’ila ya fita tare da sarkin Yahuda, da kuma sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha.

  6. Sai sarkin Isra’ila ya ce, “Mene! Ubangiji ya kira mu sarakunan nan uku don kawai yă ba da mu ga Mowab ne?”

  7. Yanzu ka duba fa, Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana shirin yă ɗauke kowane tanadi da taimako daga Urushalima da Yahuda dukan tanade-tanaden abinci da kuma dukan tanade-tanaden ruwa,