Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Water

197 ayoyi · 84 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Dole mu sayi ruwan da muke sha; sai mun biya mu sami itace.

  2. Haka ma ka auna kashi ɗaya bisa shida na garwan ruwa ka sha shi a ƙayyadadden lokaci.

  3. Kowane hannu zai raunana, kowace gwiwa kuma za tă zama marar ƙarfi kamar ruwa.

  4. Zan yayyafa muku ruwa mai tsabta, zan kuwa tsarkake ku daga dukan ƙazantarku daga kuma dukan gumakanku.

  5. Mutumin ya komo da ni zuwa mashigin haikalin, sai na kuwa ga ruwa yana malalowa daga ƙarƙashin madogarar ƙofar haikalin wajen gabas (gama haikalin yana fuskantar gabas). Ruwan yana malalowa daga ƙarƙashin gefen kudun haikalin, kudu da bagaden.

  6. Sai ya fitar da ni ta ƙofar arewa ya kewaye da ni ta waje zuwa ƙofar da take waje mai fuskantar gabas, ruwan kuwa yana malalowa daga wajen kudu.

  7. Yayinda mutumin ya yi wajen gabas da karan awo a hannunsa, sai ya auna kamu dubu ya kuma bi da ni ta ruwan da zurfinsa ya kama ni a idon ƙafa.

  8. Ya auna wani kamu dubu ya kuma bi da ni a ruwan da zurfinsa ya kai ni gwiwa. Ya sāke auna kamu dubu ya kuma bi da ni a ruwan da zurfinsa kama ni a gindi.

  9. Ya auna wani kamu dubu, amma a yanzu ruwan ya zama kogin da ban iya hayewa ba, domin ruwan ya taso ya kuma yi zurfin da ya isa a yi iyo a ciki, kogin da ba za a iya hayewa ba.

  10. Mahaifiyarsu ta yi rashin aminci ta kuma ɗauki cikinsu ta wurin yi abin kunya. Ta ce, ‘Zan bi kwartayena, waɗanda suke ba ni abinci da ruwa, ulu nawa da lilina, mai nawa da kuma abin sha na.’

  11. Shugabannin Yahuda suna kamar waɗanda suke matsar da duwatsun shaidar da aka sa a kan iyaka ne. Zan zubo musu da fushina a kansu kamar rigyawar ruwa.

  12. Gama duniya za tă cika da sanin ɗaukakar Ubangiji, yadda ruwaye suka rufe teku.

  13. Ke kuma, saboda jinin alkawarina da ke, zan ’yantar da ’yan kurkukunki daga rami marar ruwa.

  14. Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin.

  15. Sa’ad da almajiran suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai tsoro ya kama su. Suka yi ihu don tsoro suka ce, “Fatalwa ce.”

  16. Amma nan da nan Yesu ya ce musu, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”

  17. Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji in kai ne ka ce mini in zo wurinka a kan ruwan.”

  18. Ya ce, “Zo.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan, ya taka a kan ruwan ya nufe wajen Yesu.

  19. Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi.

  20. A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can,

  21. aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren.

  22. Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.”

  23. Yesu ya ce, “Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna.”

  24. Sai mahaifiyarsa ta ce wa bayin, “Ku yi duk abin da ya faɗa.”

  25. Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin.