Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The First Temple

365 ayoyi · 72 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa, ya yi sihiri da tsubu, ya tuntuɓi masu duba da masu ruhohi. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.

  2. Ya ɗauki siffar ginshiƙin Asherar da ya yi, ya sa a haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Solomon, “A cikin wannan haikali, da kuma cikin Urushalima inda na zaɓa daga kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.

  3. A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, Sarki Yosiya ya aiki Shafan ɗan Azaliya, ɗan Meshullam, magatakarda, zuwa haikalin Ubangiji. Ya ce,

  4. “Ka haura zuwa wurin Hilkiya babban firist ka sa yă shirya kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tara daga mutane.

  5. Ka sa su danƙa su a hannun waɗanda aka zaɓa don biyan ma’aikatan da suka yi gyara a haikalin Ubangiji,

  6. wato, kafintoci, da magina, da masu tsara gini. Ka kuma sa su sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu don a gyara haikalin.

  7. Amma ba sa bukata su ba da bayanin kuɗin da aka danƙa musu domin suna aikinsu da aminci.”

  8. Sai Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist, tare da firistocin da suke taimakonsa, da masu tsaron ƙofa su kawar da dukan abubuwan da aka yi domin Ba’al, da domin Ashera, da kuma domin dukan rundunar taurari, daga haikalin Ubangiji. Ya ƙone su a bayan Urushalima a filayen Kwarin Kidron, ya kwashe tokan zuwa Betel.

  9. Ya kawar da firistocin gumakan da sarakunan Yahuda suka naɗa don su ƙona turare a masujadan kan tuddai na garuruwan Yahuda, da kuma waɗanda suke kewaye da Urushalima, masu ƙona turare wa Ba’al, rana da wata, ga rukunin taurari, da kuma ga dukan rundunan taurari.

  10. Ya ɗauke ginshiƙin Ashera daga haikalin Ubangiji zuwa Kwarin Kidron can bayan Urushalima, ya ƙone shi a can. Ya niƙa shi sai da ya zama toka, sai ya watsar da ƙurar a filin kabarin talakawa.

  11. Ya kuma rurrushe mazaunan karuwai mazan haikali waɗanda suke a haikalin Ubangiji, da kuma inda mata suke yi wa Ashera saƙa.

  12. Ya kawar da dawakan nan da sarakunan Yahuda suka keɓe wa gumakan nan na rana daga mashigin haikalin Ubangiji. Waɗannan dawakan suna kusa da ɗakin Natan Melek, ɗaya daga cikin dattawan sarki. Yosiya ya kuma ƙone kekunan yaƙi a yin sujada ga gumakan nan rana.

  13. Ya rushe bagadan da sarakunan Yahuda suka kafa a kan ɗakin sama kusa da ɗakin sama na Ahaz, da kuma bagadai biyu da Manasse ya gina a filaye biyu na haikalin Ubangiji. Ya kawar da su daga can, ya farfashe su, ya zubar da tarkacen a Kwarin Kidron.

  14. Ya cinna wa haikalin Ubangiji wuta, da fadan sarki, da kuma dukan gidajen Urushalima. Ya kuma ƙone duk wani gini mai muhimmanci.

  15. Babiloniyawan kuma suka sassare ginshiƙan tagulla, da wuraren zama da za a iya matsar da su, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla da yake a haikalin Ubangiji, suka kwashe tagullan zuwa Babilon.

  16. Suka ɗauke tukwane, da manyan cokula, da acibalbal, da kwanoni, da dai dukan kayan da aka yi da tagulla don hidima a haikalin Ubangiji.

  17. Babban hafsan matsaran sarkin ya kwashe har da kwanoni na kwashe garwashin wuta da sauran kwanoni, dukansu kuwa ƙeran zinariya ko azurfa tsatsa ne.

  18. Tagullar ginshiƙai biyun nan, da ta ƙaton kwanon da ake ce da shi Teku, da ta dukan amalanke masu riƙe ruwa waɗanda Sarki Solomon ya yi domin haikalin Ubangiji, sun fi gaba a auna su.

  19. Tsawon kowane ginshiƙi, ƙafa ashirin da bakwai ne. Hulunan tagullan da suke ƙwalƙwalin kowane ginshiƙi kuma yana da tsawon ƙafa huɗu da rabi. Kuma aka yi masa ado da saƙa da ’ya’yan itace kewaye da shi. Bayan ginshiƙin ma haka yake.

  20. Shi ne zai gina gida domina, zan kuma kafa sarautarsa har abada.

  21. A lokacin, sa’ad da Dawuda ya ga cewa Ubangiji ya amsa masa a masussukar Ornan mutumin Yebus, sai ya miƙa hadayu a can.

  22. Tabanakul na Ubangiji da Musa ya yi a hamada, da kuma bagaden hadaya ta ƙonawa a lokacin suna a tudun Gibeyon.

  23. Amma Dawuda bai iya zuwa gabansa don yă yi tambaya ga Allah ba, gama yana jin tsoron takobin mala’ikan Ubangiji.

  24. Dawuda kuwa ya umarta a tattara baƙin da suke zama a Isra’ila, daga cikinsu ya sa masu farfasa duwatsu don su shirya duwatsun da aka sassaƙa saboda ginin gidan Allah.

  25. Ya tanada ƙarfe mai yawa don ƙusoshi saboda ƙyamaren hanyoyin shiga da kuma saboda mahaɗai, da ƙarin tagulla fiye da ƙirge.