Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Righteousness

480 ayoyi · 132 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba?

  2. Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba?

  3. Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya?

  4. “Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa.

  5. Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba.

  6. In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?

  7. Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’

  8. Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu.

  9. Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.

  10. Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa.

  11. Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da ’yar’uwata da kuma mahaifiyata.”

  12. “Amma da sarkin ya shigo don yă ga baƙin, sai ya ga wani can da ba ya sanye da kayan auren.

  13. Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.

  14. “Sai sarkin ya ce wa fadawa, ‘Ku daure shi hannu da ƙafa, ku jefar da shi waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’

  15. “Gama kirayayu da yawa, amma zaɓaɓɓu kaɗan ne zaɓaɓɓu.”

  16. Ta haka alhakin jinin masu adalcin da aka zubar a duniya, tun daga jinin Habila mai adalci, zuwa jinin Zakariya ɗan Berekiya, wanda kuka kashe tsakanin haikali da bagade zai koma kanku.

  17. Masu wucewa, suka zazzage shi, suna kaɗa kai,

  18. suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!”

  19. Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa,

  20. “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi.

  21. Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ”

  22. Haka ma, ’yan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi.

  23. Ya yi tambaya ya ce, “Su wane ne mahaifiyata, da ’yan’uwana?”

  24. Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi ya ce, “Ga mahaifiyata da ’yan’uwana!

  25. Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da ’yar’uwata, da kuma mahaifiyata.”