Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Righteousness: Speak contemptuously against those who follow

7 ayoyi · 132 fannoni

Ayoyi game da Speak contemptuously against those who follow

  1. Bari a rufe leɓunan ƙarairayinsu, gama da fariya da reni suna magana da girman kai a kan adalai.

  2. Masu wucewa, suka zazzage shi, suna kaɗa kai,

  3. suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!”

  4. Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa,

  5. “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi.

  6. Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ”

  7. Haka ma, ’yan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi.