- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 605–538 BC
The Babylonian Exile
Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Makoki 4:16kusan 588 K.H.
Ubangiji kansa ya warwatsa su; ya daina duban su. Ba a ba firistoci girma, ba su ba dattawa gata.
- Makoki 4:17kusan 588 K.H.
Idanunmu sun gaji, suna ta dubawa ko taimako zai zo; mu sa ido ko za mu ga ƙasar da za tă iya taimakon mu.
- Makoki 4:18kusan 588 K.H.
Ana bin sawunmu, ba za mu iya tafiya kan tituna ba. Ƙarshenmu ya kusa, kwanakinmu sun ƙare, gama ƙarshenmu ya zo.
- Makoki 4:19kusan 588 K.H.
Masu fafarar mu sun fi gaggafa mai firiya a sararin sama sauri; sun fafare mu a kan duwatsu suna fakon mu a jeji.
- Makoki 4:20kusan 588 K.H.
Shafaffe na Ubangiji, numfashin ranmu, ya fāɗi cikin tarkonsu. Muna tunani cewa za mu iya rayuwa cikin sauran mutane a ƙarƙashin inuwarsa.
- Makoki 4:21kusan 588 K.H.
Ku yi murna da farin ciki, ya Diyar Edom, ke mai zama a ƙasar Uz. Amma ke ma za a ba ki kwaf; za ki bugu ki zama tsirara.
- Makoki 4:22kusan 588 K.H.
Ya Diyar Sihiyona, hukuncinki zai ƙare; ba zai sa zaman bautarki yă yi tsayi ba. Amma ya Diyar Edom, zai hukunta zunubinki yă tona tsiraicinki.
- Makoki 5:1kusan 588 K.H.
Ka tuna, ya Ubangiji, abin da ya faru da mu; duba, ka ga kunyar da muka sha.
- Makoki 5:2kusan 588 K.H.
An ba wa baƙi gādonmu, gidajenmu kuma aka ba bare.
- Makoki 5:3kusan 588 K.H.
Mun zama marayu marasa ubanni, uwayenmu kamar gwauraye.
- Makoki 5:4kusan 588 K.H.
Dole mu sayi ruwan da muke sha; sai mun biya mu sami itace.
- Makoki 5:5kusan 588 K.H.
Masu fafararmu sun kusa kama mu; mun gaji kuma ba dama mu huta.
- Makoki 5:6kusan 588 K.H.
Mun miƙa kanmu ga Masar da Assuriya don mu sami isashen abinci.
- Makoki 5:7kusan 588 K.H.
Kakanninmu sun yi zunubi kuma ba sa nan yanzu, mu ne aka bari muna shan hukuncinsu.
- Makoki 5:8kusan 588 K.H.
Bayi suna mulki a kanmu, kuma ba wanda zai ’yantar da mu daga hannuwansu.
- Makoki 5:9kusan 588 K.H.
Muna samun burodi a bakin rayukanmu domin takobin da yake a jeji.
- Makoki 5:10kusan 588 K.H.
Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu, muna jin zazzaɓi domin yunwa.
- Makoki 5:11kusan 588 K.H.
An yi wa mata fyaɗe a cikin Sihiyona, da kuma budurwai a cikin garuruwan Yahuda.
- Makoki 5:12kusan 588 K.H.
An rataye ’ya’yan sarakuna da hannuwansu; ba a ba wa dattawa girma.
- Makoki 5:13kusan 588 K.H.
Samari suna faman yin niƙa; yara kuma suna fama da ƙyar da nauyin kayan itace.
- Makoki 5:14kusan 588 K.H.
Dattawan sun bar ƙofar birnin, samari sun daina rera waƙa.
- Makoki 5:15kusan 588 K.H.
Farin ciki ya rabu da zuciyarmu; rayuwarmu ta zama makoki.
- Makoki 5:16kusan 588 K.H.
Rawani ya fāɗi daga kanmu. Kaiton mu gama mun yi zunubi!
- Makoki 5:17kusan 588 K.H.
Domin wannan zuciyarmu ta yi sanyi; domin waɗannan abubuwa idanunmu sun dushe
- Makoki 5:18kusan 588 K.H.
gama Tudun Sihiyona ya zama kufai, sai diloli ke yawo a wurin.