Tsallake zuwa abun ciki

circa 605–538 BC

The Babylonian Exile

Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.

1,784 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Makoki 3:32kusan 588 K.H.

    Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai, ƙaunarsa tana da yawa.

  2. Makoki 3:33kusan 588 K.H.

    Gama ba haka kawai yake kawo wahala ko ɓacin rai ga ’yan adam ba.

  3. Makoki 3:34kusan 588 K.H.

    Bai yarda a tattake ’yan kurkuku a ƙasa ba,

  4. Makoki 3:35kusan 588 K.H.

    ko kuma a danne wa mutum hakkinsa a gaban Maɗaukaki,

  5. Makoki 3:36kusan 588 K.H.

    ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba?

  6. Makoki 3:37kusan 588 K.H.

    Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika in ba Ubangiji ne ya umarta ba?

  7. Makoki 3:38kusan 588 K.H.

    Ba daga bakin Maɗaukaki ne bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba?

  8. Makoki 3:39kusan 588 K.H.

    Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?

  9. Makoki 3:40kusan 588 K.H.

    Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta, sai mu kuma koma ga Ubangiji.

  10. Makoki 3:41kusan 588 K.H.

    Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmu ga Allah na cikin sama, mu ce,

  11. Makoki 3:42kusan 588 K.H.

    “Mun yi zunubi mun yi tawaye ba ka kuwa gafarta ba.

  12. Makoki 3:43kusan 588 K.H.

    “Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu; ka karkashe mu ba tausayi.

  13. Makoki 3:44kusan 588 K.H.

    Ka rufe kanka da gajimare don kada addu’armu ta kai wurinka.

  14. Makoki 3:45kusan 588 K.H.

    Ka mai da mu tarkace da juji a cikin mutane.

  15. Makoki 3:46kusan 588 K.H.

    “Dukan maƙiyanmu suna ta yin mana magana marar daɗi.

  16. Makoki 3:47kusan 588 K.H.

    Muna cika da tsoro, da lalatarwa da hallakarwa.”

  17. Makoki 3:48kusan 588 K.H.

    Hawaye na kwararowa daga idanuna domin an hallaka mutanena.

  18. Makoki 3:49kusan 588 K.H.

    Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye, ba hutawa.

  19. Makoki 3:50kusan 588 K.H.

    Har sai in Ubangiji ya duba daga sama ya gani.

  20. Makoki 3:51kusan 588 K.H.

    Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki domin dukan matan birnina.

  21. Makoki 3:52kusan 588 K.H.

    Maƙiyana suna farauta ta ba dalili kamar tsuntsu.

  22. Makoki 3:53kusan 588 K.H.

    Sun yi ƙoƙari su kashe ni a cikin rami suka kuma jajjefe ni da duwatsu;

  23. Makoki 3:54kusan 588 K.H.

    ruwaye suka rufe kaina, sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa.

  24. Makoki 3:55kusan 588 K.H.

    Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji, daga rami mai zurfi.

  25. Makoki 3:56kusan 588 K.H.

    Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka ka ƙi jin roƙona na neman taimako.”