Tsallake zuwa abun ciki

circa 605–538 BC

The Babylonian Exile

Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.

1,784 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Makoki 3:57kusan 588 K.H.

    Ka zo kusa lokacin da na kira ka, kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.”

  2. Makoki 3:58kusan 588 K.H.

    Ya Ubangiji, ka goyi bayana; ka fanshi raina.

  3. Makoki 3:59kusan 588 K.H.

    Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba. Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya!

  4. Makoki 3:60kusan 588 K.H.

    Ka ga zurfin ramakonsu, da duk mugun shirin da suke yi mini.

  5. Makoki 3:61kusan 588 K.H.

    Ya Ubangiji, ka ji zaginsu, da duka mugun shirin da suke yi mini

  6. Makoki 3:62kusan 588 K.H.

    Abin da maƙiyana suke yin raɗa a kai game da ni duk yini.

  7. Makoki 3:63kusan 588 K.H.

    Dube su! A zaune ko a tsaye, suna yi mini ba’a cikin waƙoƙinsu.

  8. Makoki 3:64kusan 588 K.H.

    Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji, domin abin da hannuwansu suka yi.

  9. Makoki 3:65kusan 588 K.H.

    Ka sa yana ta rufe zuciyarsu, kuma bari la’anarka ta bi su.

  10. Makoki 3:66kusan 588 K.H.

    Ka fafare su cikin fushi ka hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji.

  11. Makoki 4:1kusan 588 K.H.

    Zinariya ta rasa kyanta, hasken zinariya ya dushe! An warwatsar da tsarkakakkun duwatsu masu daraja a kan tituna.

  12. Makoki 4:2kusan 588 K.H.

    Dubi samarin Sihiyona masu daraja, waɗanda a dā darajarsu ta isa nauyin zinariya, yanzu ana ɗaukar su a matsayin tukwanen ƙasa, aikin maginin tukwane!

  13. Makoki 4:3kusan 588 K.H.

    Ko diloli suna ba ’ya’yansu nono su sha, amma mutanena sun zama marasa zuciya kamar jiminai a cikin jeji.

  14. Makoki 4:4kusan 588 K.H.

    Domin ƙishirwa harshen jarirai ya manne a rufin bakinsu; yaran suna roƙo a ba su burodi, amma ba wanda ya ba su.

  15. Makoki 4:5kusan 588 K.H.

    Waɗanda a dā sukan ci abinci mai daɗi yanzu su ne masu bara a tituna. Waɗanda a dā suke sa kaya masu kyau yanzu suna kwance a kan tarin toka.

  16. Makoki 4:6kusan 588 K.H.

    Horon mutanena ya fi na Sodom girma, wadda aka hallaka farat ɗaya ba wani hannu da ya juya ya taimake ta.

  17. Makoki 4:7kusan 588 K.H.

    ’Ya’yan sarakunansu sun fi ƙanƙara haske sun kuma fi madara fari, jikunansu sun fi murjani ja, kyansu kamar shuɗin yakutu.

  18. Makoki 4:8kusan 588 K.H.

    Amma yanzu sun fi dare duhu; ba a iya gane su a tituna. Fatar jikinsu ta manne da ƙasusuwansu; sun bushe kamar itace.

  19. Makoki 4:9kusan 588 K.H.

    Gara waɗanda aka kashe su da takobi da waɗanda suke mutuwa da yunwa; sun rame domin rashin abinci a gona.

  20. Makoki 4:10kusan 588 K.H.

    Da hannuwansu mata masu tausayi sun dafa yaransu, suka zama masu abinci sa’ad da aka hallaka mutanena.

  21. Makoki 4:11kusan 588 K.H.

    Ubangiji ya saki fushinsa; ya zuba zafin fushinsa. Ya hura wuta a Sihiyona ta kuma cinye harsashin gininta.

  22. Makoki 4:12kusan 588 K.H.

    Sarakunan duniya ba su gaskata ba, haka ma mutanen duniya, cewa magabta da maƙiya za su iya shiga ƙofofin Urushalima.

  23. Makoki 4:13kusan 588 K.H.

    Amma ya faru domin zunuban annabawanta da muguntar firistocinta, waɗanda suka zub da jinin masu adalci a cikinsu.

  24. Makoki 4:14kusan 588 K.H.

    Yanzu suna yawo barkatai a tituna kamar makafi. Sun ƙazantu da jini yadda ba wanda zai kuskura ya taɓa rigunansu.

  25. Makoki 4:15kusan 588 K.H.

    “Ku tafi! Ba ku da tsabta!” Haka mutane suke ihu suke ce musu. “Ku tashi daga nan! Ku tashi daga nan! Kada ku taɓa mu!” Sa’ad da suka gudu suna yawo, mutanen waɗansu ƙasashe suka ce, “Ba za su ci gaba da zama a nan ba.”